Posts
Showing posts from February, 2020
Ta'addancin Jami'an Tsaron Yan Sanda a Akan Masu Muzaharar #FreeZakzaky Sun Kashe Mutum Daya a Kaduna! Kamar Yanda Suka Saba Yan Uwa Almajiran Sayyed Zakzaky Dake Garin Kaduna Sun Fito Domin Gabatar da Muzaharar Lumana ,Domin Cigaba da Jaddada kira Ga Azzalumar Gwamnatin Buhari data Gaggauta Sakin Sayyed Zakzaky Daga Tsarewar Zalumcin da take Masa Fiye da Shekara Hudu Bisa Zalumci. Yan Uwa Sun Fito Dauke da Pastoci Da Kwalaye Suna tafiya Suna Slogans Na Kiraye kiraye akan Gwamnatin Buhari taji Umarnin Kotu ta Saki Shehin Malamin Kamar Yanda Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta bayar da Umarnin Hakan Fiye da Shekara Uku kenan ,tun Ranar 02/12/2016 Jami'an Tsaron Yan Sanda Hadin Gwuiwa da Yan kato da Gora Sun Farwa Masu Muzaharar Lumana da Harbin Bindiga da Harsashi Mai Live akan Me Uwa dawabi. Wannan Harin Ta'addancin da Jami'an Tsaron Yan Sanda Suka kawo yayi Sanadiyyar Kashe Mutum Daya ,Me Suna :Jawad Ameen Liman tare da Kama Wasu Ciki Harda Mata ,Bayan Sun jikkatasu Da Rauni, Kuma Sun Tafi Dasu Suna Tsare dasu Bisa Zalumci Batare da Kulawaba . Ba Wannan ne karon Farko ba Da Gwamnatin Jahar Kaduna take Afkwa Almajiran Sayyed Zakzaky Idan Sun Fito Gudanar da Fahimtar su Na Addini ,tare da Qalubalantar Wannan Zalumcin da Gwamnatin Buhari takewa Harkar Musulumci da Jagoranta Sayyed Zakzaky. Ko' a Lokacin #MuzaharAshura2019 Sun Afkawa Yan Uwa Inda Suka Kashe Mutum Uku tare da Raunata Daruruwan Yan Uwa. Gwamnatin Nigeria dai Na Tsare da Sayyed Zakzaky Ne Fiyr da Shekara Hudu ,Tun Bayan Harin Ta'addancin da Sojojin Buhari suka Kaddamar akan Sayyed Zakzaky da Almajiran sa ,a ranar 12-14/Dec/2015 Harin da Yayi Sanadiyyar Kashe Sama Da Mutum 1000+ Ciki harda Yayan Sheikh Guda Uku. #FreeZakzaky #DeathToBuhari #DeathToRufa'i Hydar Mahmoud Dandume 26/Feb/2020
- Get link
- X
- Other Apps