WANNAN TUNATARWA CE

WANNAN TUNATARWACE


Na taba ji Sheikh Zakzaky yana cewa; shi Aure anayin sa idan akwai Soyayya tsakani, don haka ne ma yasa kafin ayi Aure, ake son ya zama cewa akwai Soyayya tsakanin su, ya zama cewa sun san halin junansu, su samu fahimtar juna kafin Aure. Saboda gudun kar ayi Auren ya zama ana samun matsala.


Kuma na taba ji Sheikh Zakzaky yana cewa ita Yarinyar da za a aurar tanada hakkin atambayeta idan tana son auren,idan kuma ta ce bata so sai akyale ta,

Sannan na Tambayi wani Malami na dangane da al'amarin neman aure, sai yake ce mun lallai a Mazhabin Ahlulbayt baya Halatta ayiwa Mutum Auren dole.

Kuma na tabaji wani Babban Malamin mu yana cewa, kai koda antaru ne ana daura Aure,sai ita Yarinyar ta ce ta fasa Auren,to dole ne afasa daura Auren,har sai ranar da Yarinyar ta Amince. Amma su iyaye su tabbatar da cewa shi mutumin kirki ne, shi ma ya tabbatar da cewa Yarinyar kirki ce..

Sheikh Zakzaky ya ce;ni ban san anayin Aure idan babu Soyayya ba, kuma ban san anayin Aure don wani abin duniya ba, abinda na sani shine ana ba mutun aure idan ya kasance mutumin kirki,indai har yanada sana'ar da zai iya fita ya nemo abincin da zasu ci,to babu laifi,ana iya bashi Aure. Amma bawai sai yanada wai abin duniya ba, ana mutum Aure ne idan mutumin kirkiki ne.

Comments

Popular Posts