ABINDA NA FAHIMTA GAMEDA WANNAN CUTA TA CORONAVIRUS WACCE AKAFI SANI DA COVID-19.
wannan cuta Allah yajarabci mutanen duniya ne da ita wanda yake da munajinta acan nesane sauran kasashe, har takaiga ayanxu ta tsallako cikin wannan kasa tamu wacce ake cewa Nigeria. Na'am wannan cuta babu musu akwaita amma matsalar saidai abubuwan daka iya biyo baya marasa dadi Allah yakiyaye.
Nafarko shine anan kasar tamu yanda ake zuzuta CUTAR maganar gsky batakai hakaba. Kullum Ana zuzutata Ana tsorata talakawa bayada babu wani yunkuri Na gaske da akeyi Dan dakileta (domin ko shugaban kasa sai shekaran jiya-jiyama ya iya futowa yayi mgn bayada tama kama kusan mutum talatin da uku. Wanda adadinta yakai kimanin mutum 40.)
Anan kasar kowa yasani cewa bamu da wani kwararren asibitin da xamu iya fuskantar wannan cutar dashi idan mukayi la'akari da sauran kasashen da suke da manyan asibitoci ya suka karke da ita?.
Wanda kowa yasani kuma shedane cewa su kansu shuwagabannin kasarnan basuyarda da asibitocin kasarba ko ciwon kai kedamunsu basa tsayawa adubasu agida saidai su saka kafa su tsallake domin me? Saboda babu kwararrun kayan aiki bakuma a maida asibitocin komaiba.( yanxu masifarma shine su masu SA kafa sufita domin jinya yanxu babu dama saidai kowa yaxauna agida Dan dole yagirbi abinda ya shuka.)
Haka idan kahau kafar sadarwa babu abinda xaka rika gani sai labaran an Hana xuwa masallaci ko za'a Hana sallar jam'i kullum abinda xakayi taji kenan daxarar kaji an Hana Abu to wurin ibada xakaji ( kai kace wannan cuta taxo tayaki Islam ne).
Abin takaicine ace musulmi saboda tsoron wata cuta ko wani Abu xai iya Jin tsoron AIKATA ayyukan ibada ba.
Abin tambayar shine idan masallaci da sallolin jam'i sun xama abin barazana agun musulmi saboda tsoron kamuwa da wannan cutar inaga sauran wurare? Sannan ina tauhidinshi yake? (Xamu fahimci gskyne idan mukayi la'akari da sauran kasashen dasuka ce baxasu Hana xuwa masallaci Dan wai kar adau cutaba ).
Masu cuta kabasu sauki mukuma ka kuremu
Comments
Post a Comment