SHEKARU FIYE DA HUƊU DA KISAN KIYASHIN ZARIYA: Muna Bin Gwamnatin Buhari Bashin Jinainan Ƴan Uwanmu!
Daga: Sunusi Alhassan Sufiy
Bawan Allahn da tun fiye da shekaru 4 aka zalunce shi, zalunci marar misaltuwa. An kashe masa ƴaƴayensa na cikinsa har guda 3. An harbe yayarsa mai suna Gwaggo Fatima (Gwaggan Ƙaura) saboda tsabar zalunci, ba kuma tare da sun taka wani haƙƙi na shari'a ba. Ko a dokokin ƙasa-da-ƙasa ne ma abin da gwamnatin Buhari tasa aka yiwa ƴan Shi'a a birnin Zariya a shekarar 2015 ya saɓawa dukkan wani ƙa'ida! Ko baku faɗi kyawawan ayyuka na alkairin da Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) ke yiwa ga ɗimbin al'umma ba, hidimtawa ga mabuƙata, taimakon gajiyayyu da kuma ɗabbaƙa kyawawan ayyukan da yake na isar da kyawawan ayyuka da saƙon da addinin Islama ya koyar da al'umma ba; bai kamata kuma ku ƙulla masa sharri, ƙage da munanan kalamai don cin zarafinsa tare da ƙoƙarin biyawa iyayen gidanku da kuma buƙatun kawukanku ba. Ko Buharin da kuke ganinsa ɗan kwangila ce daga ƙasashen waje. Aiki aka bashi, don ganin ya kawo ƙarshen numfashin Shaikh Zakzaky (H) da da'awarsa! Yana daga cikin sharuɗɗan danƙamasa mulki a hannunsa don ya kawo ƙarshen Shaikh Zakzaky (H).
Na tabbata idan da ace abin da aka yiwa waɗannan bayin Allah (Shaikh Zakzaky da mai ɗakinsa Malama Zeenah) waɗansun sune aka yiwa haka da tuntuni ƙasar ta dade da canza salo da kuma yanayi na halin da yanzu ake ciki. Me kake tsammanin zai biyo baya daga mabiya waɗannan mutane? Ƙiri-ƙiri al'umma sun san an zalunce su, amma sun ja bakunansu sun yi shiru. Saboda su a tunaninsu tun da zaluncin bai iso ga kawukansu ba, ƴan uwansu da dangi suna zaune cikin ƙoshin lafiya tare da walwala: kaga ai wannan ba komai bane. Basu damu da kowane irin hali zai kasance a ciki ba, duk da cewa akwai waɗanda dama tun farkon faruwar al'amarin sun nuna baƙin ciki da takaicinsu akan abin da aka yiwa ƴan Shi'a a birnin Zariya. Babu yadda suka iya ne kawai addinin Musulunci ba jahilci bane, bai kuma taɓa koyi da umarni da dukkan wasu ayyuka irin wanda gwamnatin Buhari tasa aka yiwa ɗaruruwan ƴan Shi'a a Zariya ba! A bisa umarnin gwamnatinsa ne aka kashe tare da ƙonawa, a mulkinsa ne akaiwa mamata ƙabari na-bai-ɗaya. Ko labarin hakan bai iso gareku ba? Sai ka tambayi kanka, wai shin abin da gwamnatin Buhari ta yi akan waɗannan mutane, wane irin zalunci ne haka!? Idan har waɗansu nada bakin iya magana akan waɗansu rayuka da ake kashewa a wasu ƙasashen, kuma duniya ta ji; me yasa basa tallatawa duniya kisan kiyashin da ya faru a ƙasarsu?
Su kuwa waɗanda muguwar soyayyarsu da Buhari ta rufe masu idanuwansu, sun doɗe ƙwaƙwalensu waje guda tare da nuna gazawarsu a sarari, su fitowa fili su faɗawa duniya da kuma gwamnatin Buhari gaskiya kan al'amarin kisan ɗaruruwan musulmai fiye da 1000+ a Zariya sun gaza, ko sun manta cewa akwai ranar karɓar sakamako a wajen Allah (T) ne? Akwai ranar da mutum zai yi nadama marar amfani da kuma da-na-sani ta har abada ba zai taɓa amfanarsa ba?! Ya kamata al'umma ku yi nazari da tunani! Yaushe ran ɗan Adam ya zama abin kashe da zalunta, ban da a gwamnatin da sam-sam bata san mutuncin kanta da haƙƙin waɗansu ba! Allah (T) ba azzalumin bayinsa bane, da yawa waɗansu bala'o'in da suke faruwa damu, sakamakon munanan ayyukanmu ne suka sabbaba mana haka. Shi aka zalunta, aka rushe masa muhallai da wuraren ibada. Baya ga haka, an tsare shi na tsawon shekaru fiye da huɗu, a lokaci guda kuma yana fama da rashin lafiya na rauninda miyagun sojojin Najeriya suka yi masa! Wannan zalunci da me ya yi kama?
Al'umma kuyi mana adalci bisa abin da gwamnatin Buhari ɗin nan tayi mana. A ko'ina muna faɗa. Mun kuma maimaitawa, zamu ci gaba kuma da maimaitawa har ƙarshen numfashinmu! Gwamnatin Buhari ba gwamnati ce wanda take wakiltar addini ba, ba kuma wakiltar Allah (T) da dokokin Musulunci take yi ba, saboda babu addinin da ya ce aje a kashe mata da ƙananan yara haka kawai saboda sun saɓawa wata fahimta, duk mai aikata irin hakan kuwa ba addini yake wakikta ba; kawai yana bin son ransa ne. Ya sani, ko bai sani ba. Gashi kuma ita kanta gwamnatin ta gaza fitiwa fili ta ƙaryata abin da ake faɗi akanta, ta kuma kasa nunawa duniya cewa ita gwamnati ce wanda bata taɓa alfahari tare da mutunta dokokin ƙasarta ba. Ya bayyana a fili, ba kuma a shirye suke da su bi umarnin da wata babbar Kotu dake birnin Taayyar, Abuja dake Najeriya ta bayar na sakin Shehin malamin da mai ɗakinsa, a shekarar 2016 ba. Ba iya waɗannan shekaru bane Kotu na bayar da umarni kan al'amarin Shaikh Zakzaky (H) ba, ga kuma rashin lafiyar da suke fama tare dashi da mai ɗakinsa na irin miyagun raunukan da gwamnatin Buhari tasa aka yi masu a Gyallesu, Zariya ba. Idan gwamnatin Buhari na taƙama da mulki ne, an yi waɗanda suka gabace shi. Sun wuce, yanzu suna ina? Sun zama tarihi. Muna fatan shima haka zai zo ya wuce, wannan kamar yanzu ne a wajen Allah (T).
Sunnar Allah, bata canzawa, haka magabata suka sha fama da azzalumai masu mulki na waɗancan lokutan. An nemi ganin bayansu tare da kuma abin da suke kira akai, Allah bai yarje masu ba. Dukkan waɗanda suka bi tafarki madaidaiciya sai Allah ya jarabcesu da jarabawoyi kala-kala. Muna fatan Allah ya ƙara mana juriya da sabati bisa hanya na gaskiya!
Comments
Post a Comment