JAGORA (H) YAYI WATSI DA TAYIN MAGANIN CORONA DA AMURKA TA YI WA IRAN

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya al’ummar musulmi na duniya murnar zagayowar ranar da aka aiko Annabi Muhammadu (s.a.w.a) a matsayin Annabi kuma manzo.
Jagoran ya bayyana hakan ne cikin jawabin sabuwar shekara da a halin yanzu yake ci gaba da yi ga al’ummar Iran don taya su murnar shigowa sabuwar shekarar 1399 hijira shamsiyya da kuma ranar da aka aiko Annabi (s.a.w.a) wacce ta fado a yau.
Yayin da yake magana kan ranar da aka aiko Annabi (s.a.w.a) a matsayin manzo, Jagoran ya bayyana cewar aiko Annabi da kuma sakon da ke cikin hakan wani lamari ne mai amfani hatta ga wannan zamani da muke ciki. Don kuwa sakon Annabin wani sako ne da ya bayyanar wa al’umma da hakikanin lamurra da kuma gaskiya, wanda idan bil’adama suka yi riko da wannan sako lalle za su sami rayuwar da ta dace da su.
Yayin da ya koma kan batun cutar nan ta Corona kuwa, Jagoran ya sake kiran al’umma da su kara kula da kansu da kuma girmama maganganun kwararru kan hanyoyin da za a bi wajen magance wannan cutar.
Har ila yau kuma yayin da yake magana kan ikirarin Amurka na taimaka wa Iran da magungunan wannan cutar matukar dai ta bukata, Jagoran yayi watsi da wannan bukata yana mai cewa: Da farko dai ita kanta Amurkan tana bukatar maganin don haka maimakon ta yi tayi wa wani kamata yayi ta magance matsalar rashin maganin da take fuskanta.
Har ila yau kuma Jagoran ya ce Amurkan ba abar yarda ba ce don haka babu yadda za a yi Iran ta amince da ita wajen karbar magani daga wajenta yana mai cewa ta yadda za a yi a yarda da Amurka alhali ma ana zargin cewa ita ce ta kirkiro cutar
A nan gaba za mu kawo muku karin bayani kan jawabin na Jagora

Comments

Popular Posts