KO DA MAI ABIN DAUKA DAGA WANNAN IRSHADIN NA JAGORA
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yayin da yake ba da misalin yadda halin Jahiliyyar Larabawa yake, yake cewa:
"Su fa (Jahiliyya) gardama da takobi ake rabawa. Idan (misali) wani yace Malam Turi dogo ne, wani yace A'a, ai gajere ne. Aka fara fada, sai daya ya zaro takobi kawai, yace ya nace maka gajere ne za ka ce min dogo ne!? To sai a fara sara, shar-shar, (ta wannan fadan) sai a gane waye me gaskiya. Wanda ya mangare wani ya tsinke kansa shikenan an gama, Kaga Malam Turi gajere ne. (Dariya).
Jagora (H) ya kara da cewa: "Wato wani wauta, idan misali ka iya mangare wani, kai ke da gaskiya kenan? Amma su (a Jahiliyya) kawai ana sasanta tsakani ne ta hanyar takobi."
Lokacin da na ji wannan jawabin na Jagoranmu (H) da ya gabatar a wajen Mauludin ManzonAllah (S) da yan uwa na Resource Forum suka gabatar a Kaduna a shekarar 2013, sai nake cewa ikon Allah! Dama na sha fadawa mutane cewa babu wani abu da Jagoranmu bai haska mana shi ba, sai dai in mutum bai kai ga jinsa ba kawai.
A daidai lokacin da rigima ke neman kaurewa tsakanin yan uwa, musamman ma 'yan babban birni a kan Shahada ko rayuwar Malam Turi. Mu da muke da addini, muke kira gareshi ma, anya ya dace mu zama shigen Jahiliyyar Larabawa kuwa?
Ashe ba za mu zama wayayyu ba? Kawai in wani yace Malam Turi ya yi Shahada ya ba da dalilinsa, shikenan sai a bar shi ya tafi da wannan ra'ayin nasa. In wani yace Malam Turi na nan da rai bai yi Shahada ba, ya ba da hujjojinsa, shikenan kawai shima a bar shi da ra'ayinsa, mene na rigima har da shirin fara kai duka?
Tabbas ina ganin kamar akwai darasin dauka sosai daga wadannan zantukan na Jagoranmu ga dukkan bangarorin 'yan uwa akan wannan matsalar da ke neman nuna mutane a matsayin Jahiliyya, saboda jayayyarsu da husumarsu da ke neman zama doke-doke a zahiri. Ba a kan lamarin Malam Turi ba, akan komai ma 'yan uwa mu kiyayi zama daga cikin Jahiliyyar Nijeriyawa.
— Saifullahi M. Kabir
Comments
Post a Comment