AKWAI HAKKIN MANZON ALLAH (S) A KAN MU!

AKWAI HAKKIN MANZON ALLAH (S) A KAN MU!

Akwai haqqin Manzon Allah (S) a kan mu, wanda yake cewa, ‘Balligu anni walau aya,’ “ku isar min ko da aya ne.” Isarwa, kyakkyawan isarwa shi ne, ka isar da kyakkyawan aiki, domin aiki ya fi magana fiye da lafazi! A gan ka, a ga addini. A ji maganarka, a ji maganar addini. A yi hulda da kai, a ga addini. Idan aka ji kana surutun addini, kana ‘tarrrrr-tarrrrrr,’ ‘an’ wane ‘an’ wane, ‘qala’ kaza, ‘an’ wane ‘an’ wane, sai ka ci amana, ka yi murdiya, ka qara da sata, ka yi yaudara, to ka ga ina addini yake? Saboda haka a gan ka, a ga siffar addini. A yi magana da kai, a ji maganar addini. A yi hulda da kai a ga addini. A ga kai mai gaskiya ne, mai riqon amana ne, mai kawaici ne, mai dattaku ne, mai kunya ne, mai dabi’o’i kyawawa, yawwa.

Daga littafin “SABON SALON YAQI DA MUSULUNCI!” Na Cibiyar Wallafa da Yada Jawaban Shaikh Zakzaky (H).

—Jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a rufe Muzahara Maulidi ta ranar 17 ga Rabi’u-Auwal 1436- 2014, a filin Polo Zariya.

Comments

Popular Posts