IDAN MUKA DAUKI AYYUKAN HARKAH ISLAMIYYA KAMAR DAUKAR JINKA NA TABBATA MALAM ZAKZAKY(H) ZAI YI ALFAHARI DAMU...............!!!

Idan ka leka Masallaci ka ga wani a tsaye rike da microphone Yana pre-khutba ko ka fito waje ka tarar Yana post-khutba ka San tabbas ba shi kadai ya hada kayan sautin da sauran abubuwan da ake amfani dasu a wurin ba...
Idan ka ga an fito Muzaharar Ashura, Mauludi ko Free Zakzaky ana tafe ana slogan har ma da raba articles, sannan a fara ta lafiya ba tare da wasu sun yi abinda ya sabawa manufar Muzaharar ba,to ka tabbata Mutane da yawa sun taimaka wurin Samar da haka..
Mutane da yawan gaske ciki har da Azzaluman da suke kashe mu da karnukansu sukan Sha mamaki idan suka halarci programs dinmu,wadansu ma cewa suke yi idan Gwamnati ce zata shirya irin Wannan sai dai ayi budget na musamman, aikin mutum daya ne ya Samar da haka.?
Idan azzalumai suka Kama dan-uwa suka tafi dashi police station ko suka gurfanar dashi a gaban kotu ba dukkan 'yan-uwa ne zasu dunguma su bi sawu ba,wadansu ne suke zuwa...
Muna da fora dabam-dabam wadanda suke kula da ayyukan Harkah dabam-dabam domin cigaban Harkah Islamiyya karkashin jagorancin Malam Zakzaky(H)..
Na sani kaima ka sani akwai wadanda idan su zasu biya kudin mota dana bukatar yau da kullum a wurin programs na tabbata ba zasu iya zuwa ba, taimakon wasu ne yake Kai su...
Muna da makarantu da markazozi har da Hussainiyyoyi na tabbata ba dukkan mu ne muke ayyuka a wurin ba,wadansu daga cikinmu ne...
Me zai hana mu taimaka wa raunana irina domin mu samu karfin gwiwa mu Kuma karfafa jaruman mu domin a gudu tare a tsira tare.?
Kamar yadda ba kowane yake iya isar da sakon Harkah ta hanyar wakokin gwagwarmaya ba, hakanan ba kowa zai iya rubuce-rubucen isar da sakon Harkah ba...
Allahu Ta'ala ya tausaya Mana ya kwato Mana
jagoranmu daga hannun azzalumai alfarmar Annabi Muhammadu(S) da Ahlulbaitinsa(AS)....

Share linkπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘

https://ansarulmahdi.blogspot.com/

Comments

Popular Posts