SUNACIGABA DA CUTAR DASU SAYYAD ZAKZAKY {H} HAKA ZAMUSAMUSU IDO KENAN?

SUNACIGABA DA CUTAR DASU SAYYAD ZAKZAKY {H}
Wd'an marasa mutuncin wad'an da basu san me ma ake kira tausayi ba, wad'an da a sufa ne kawai suke mutane ammabdabbobi ma sun fisu daraja, basu da niyyar subar Jagoran mu Allama Sayyid Zakzakiy (H) ya rayu, kawai suna fad'ar mana ala'kawari ne don su samu su daddan ne motsin da suke ganin yin sa zai zame musu barazana, aciki da woje a 'kasashen duniya. Kamar yadda al'kur'ani ya fad'a mana gaskiyar lamari game da halayyan su cewa "...Suna fad'a ne kawai da baki don su samh ku yarda da su, alhali abin da zukatan su ke son aiwatarwa daban..." (Tauba aya ta 8.).

A lura za'a ga duk lokacin da suka fahimci an dauki wasu matakai da zasu kai ga ayi nasarar ceto rayuwar su Abba (H), sai su fito da wata yaudara, wadda sai sun yi yadda zasu donkofe wan nan yun'kurin, san nan su jefa ma 'yan'uwa jin cewa ai komai ma ya zo 'karshe, duk yadda zaka yi da 'yan'uwa bazasu fahimceka ba, kuma anyi wan nan ba sau daya ba- ba sau biyu ba.

Ko da yaushe wad'an nan kurayen birrai, kawai suna neman wani dalili da zai sa su ci gaba rik'e Jagora (H), don su kai gamanufar su ta kisa a kai-kai ce ba kai tsaye ba; shi kenan sai su ce, kashi! gashi ana cikin 'ko'karin a fita da shi amma ya cika, rai ya yi halin sa. Kamar yadda Sayyida da kan sa ya fada alokacin da suke shirin canza masa masauki daga Abuja zuwa Kd. Cewa: "...jama'a su sani wad'an nan mutanen kisa kawai suke nufi..."!

Don haka yanzu kawai yanrage ga muminai wad'an da suke amsa kiran mazlumi da yake cewa: "ya ku al'mmar Musulmi!, ina 'yan'uwa na Iamni!!, ya ku masu 'yanci na duniya?!!!.

Wad'an mutanen sun raunani, yanzu kawai ya ma rage su kasheni, shin akwai mai taimaka mini?!" ya rage duk wani matakin da ya dace wanda ta hanyar shi ne za'a ceci rayuwar Jagoran shiriya, a dauka, san nan ayi amafani da duk wani salon da ya sa'ba ma na wad'an nan ma yaudaran, maciya amana, ma'karyata don a woce inda ake.

Don gaskiyar magana babu sauran dogaro ga mutanen da basu san dangataka da zumunci ba, kamar yadda al'kur'ani ya sifaita su. (Tauba aya 8).


*"Kuyi aiki da sannu Allah da manzon sa, da muminai zasu gani.*

Comments

Popular Posts