Yana da Muhimmanci
Da ace akwai wata hanya tubus tubus wadda za abi a tsira ba wannan ba, da tuni Jagoranmu Shaikh Zakzaky (H) ya bi wannan hanyar. Da ace akwai wani yanayi da idan aka shiga cikinsa za a iya canzawa daga wata hanya zuwa wata, da su Jagoranmu (H) tuni sun canza zuwa abinda yafi dacewa. Da ace halin kunci da takura da zaluncin azzalumai, da nau'in shiga musibobi daban daban da fuskantar wahala da kalu balen rayuwa zai iya sa wa a canza kuma a samu mafita, da su Jagoranmu (H) sun canza daga halinda suka samu kansu zuwa abinda yafi zama alkhairi a garesu.
To, amma babu wannan hanya din mai tubus tubus din, hanyar kenan kwara daya rak. Itace wannan da suke a kai, a kanta suke tun ran gini tun ran zane. A wannan hali da yanayi da wadannan azzalumai suka saka wadannan bayin Allah ciki, a haka su Jagora suka daure suka dake a kai, har suka fada masu cewa idan yaso idan suna da Jahannama ta su sukai su, ba za su taba canzawa daga abinda sukai imani a kansa ba. Kuma sun fada cewa da wadannan azzaluman za su ba su sharadin cewa su dauki hannun su na dama su maida shi zuwa bamgaren hagu a madadin sharadin idan suka yi hakan za a sake su, su Jagoranmu (H) suka ce ba za suyi hakan ba, saboda zai zama sun dauki kaskanci idan suka yi, su kuma ba za su taba daukar kaskanci ba.
Ya jama'a da wane irin sifa ta bayin Allah za mu kwatanta wannan bawan Allah? Sanin hakikanin matsayin wannan bawan Allah sai dai Ubangijinsa. Ba muda wani uzurin rashin taimakawa wannan bawan Allah da duk abinda muke da shi, wannan duniya tana fuskantar babban hadari mai girma na rashin taimakon wannan bawan Allah, mafi girman hadarin kuma shine na wadanda suka san Jagoran suka gaza taimaka masa. Allah (T) kasa da mu a cikin mabiya wannan bawa naka har karshen rayuwa.
Comments
Post a Comment