Fara Da’awarsa :Shaikh Ibraheem Zakzaky
(H) ya fara wa’azi a bainar jama’a ne a wani babban taro da aka yi a makarantar “Provincial Arabic School” da ke unguwar Kwarbai a cikin birnin Zariya. Wannan taro an yi shi ne a watan Afrilu na shekarar 1972 don kafa qungiyar samarin Musulmi, kuma ya hada manyan mutane ciki har da sarakunan gargajiya. Wannan shi ne wa’azi na farko da Shaikh Zakzaky ya fara yi a bainar jama’a, a lokacin yana da shekaru 19 kacal a duniya.
To, amma Da’awa ta fikirar Harka Islamiyyah, wato kiran mutane zuwa ga bin koyarwar addini da qauracewa tsarin jahiliyya, ya fara shi ne a shekarar 1977, wato tun bai fi shekara daya a Jami’ar ABU ba, sai dai a lokacin yana Da’awa ta sirri ne ba tare da shelanta manufarsa a fili ba (Da’awa Sirriyya). Ya shafe shekaru uku a wannan mataki na Da’awa ta sirri (1977-1979), sa’annan daga baya ya shelanta manufar Da’awarsa a fili a farkon shekarar 1980 a Funtuwa.
Shaikh Zakzaky (H) ya shelanta Da’awarsa da manufarta a fili ne cikin watan Jimada-Ula na shekarar 1400 Hijira, wanda ya yi daidai da watan Yuli (?) na shekarar 1980.
Ya shelanta wannan Da’awa ne a wani babban taro na qungiyar dalibai musulmi ta qasa “Muslim Students Society” (MSS) a garin Funtua. A jawabin ya shelanta miqa wila’arsa ga Allah da Manzo (S), tare da Bara’a ga duk tsarin da ya savawa nasu, ya kuma shelanta qyamarsa ga zalunci da azzalumai. Wannan bayyana Da’awa da ya yi ita ake kira “Shelar Funtuwa” wato “Funtua Declaration” a turance.
Bayan shelanta Da’awarsa a taron dalibai na Funtuwa, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi wa’azinsa na farko ga al’umma ne a wani gangamin wa’azi da aka yi a masallacin Kwarbai dake Zariya a cikin watan Rajab na shekarar 1400 Hijira (1980), wanda shi ne wa’azi na farko xauke da fikirar Harka Islamiyya da Sheikh Zakzaky (H) ya gabatar wa mutanen gari.
Bayan shelanta wannan qira nasa ya fuskanci tsangwama mai tarin yawa ta fuskoki da vangarori da dama, kama daga azabtarwa daga vangaren hukuma, da kuma matsin lamba daga dangi da makusantansa. A wani jawabinsa yana cewa; “Wani ma ya ce min “ba za ka koma Jami’a ka yi karatu ba!” (sai) na ce masa; to ai wannan aikin da kake so na yi akwai masu yi, amma wannan (Da’awa) da nake yi ba mai yi! Saboda haka gara wannan shi ma a tsaya a yi shi” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 18).
Comments
Post a Comment