Yanzu hatta makiya addini sun tashi haikan domin bata sunan addini,ba don komai ba sai domin sunga shi addinin yana tashi.

to sai suna nunashi a mummunan kama,cewa shi tashin hankaline da kashe-kashe saboda haka makiya addinin nan sunata faman dashe-dashen bama-bamai suna cewa wai masu neman tabbatar da addinin Musuluncine sukeyi,domin a samaka kyamar addini din ya dinga tsoron addinin ya dinga kyamar addinin cewa wai ana kashe mutane.

wai sai ace wai masu kashe mutanen nan wai manufarsu zasu tabbatar da addinin Musulunci,wannan hankali ba zai iya dauka ba,kai da kake neman ka tsamar da mutane kuma sai kadinga kashesu,in kashesu ai sun mutu a azaba kenan.

wato da ganganne wannan kuma ya zama ruwan dare ba za a taba bude gidan telebijin ana labaru ba a tunantar dakai Musulmi miyagune masu kashe-kashen kawukane ba

Amma imma akwai wani musulmi mai kashe-kashe to su makiya su suka shukashi,dubi tushensa kagani daga ina ya yo asali?imma akwaishi ballantanama cikin wanda suke wasa da hankalin mutane ba wasu da suke wannan abu ba sai makiya addinin Musulunci keyi su dorawa al'ummar musulmi.

Wato ana nuna maka shi Musulunci nan abin tsorone Karka saurareshi domin kashe mutane yakeyi.

To Musulunci ba kashe mutane yakeyiba tsamar da mutane daga halaka yakeyi,kuma musulmi tsamar da mutane daga halaka yakeyi indai musulminne.

Na'am nasan akwai wasu wanda su basuma san inda addinin yasa gababa amma sun sa rigar addini kuma daga maganganun su zakaji banda jafa'i da miyagun maganganu da fishi wanda bai kama da wa'azin annabi ba,to sai suce ga wa'azin Annabi.

Acikin tafsirin Suratul Jathiya.

Sheikh Ibrahim Zakzaky(H)

Comments

Popular Posts