SHAIKH ZAKZAKY: DAN FURSUNAR DA DUNIYA TAYI SHIRU A KANSA!


Allah Sarki! Mahukunta a Nigeria na ci gaba da zaluntar Shaikh Ibrahim Zakzaky amma duniya tayi shiru musamman kasata Nigeria! Abinda ya dami Azzalummai bai fi COVID-19 da suke amfani da ita ba wajen wawure kudin Nigeria !

Ci gaba da tsare wannan bawan Allah da mai dakinsa a irin yasassun gidan yarin Nigeria abun damuwa ne sosai,musamman a mawuyacin halin da duniya ta tsinci kanta a ciki na annobar COVID-19!

A irin tsabtataccin wurare tayi mummunan barna ina ga tamu kazamtattun gidajen yari irin na Kasata Nigeria!

Shaikh Zakzaky na fama da matsananciyar rashin lafiya shi da mai dakinsa sakamakon harsasai masu guba da aka amfani da su a kansu a hare-haren ta'addancin da Buhari ya aiwatar a Zariya a ranekkun 12,13,14 ga December 2015!

Muna kira da babbar murya ga Gwamnatin Manjo Janar Buhari da ta gaggauta sakin wannan bawan Allah musamman wannan matsanancin lokaci da babu wanda yake da tabbas balantana aminci!

Muna kiran mahukunta a Nigeria kamar yanda suke kokarin rage cunkoson yan fursunar kasa da kashi 70 cikin dari a matsayin hanyoyin daqile wannan cuta ta COVID-19,da su waiwaya su tuna cewa Kotunsu karkashin jagorancin alqalinsu da suke yiwa albashi Mr.Gabreal Kolawole tun a shekarar 2016 ya bada umurnin sakin wannan bawan Allah ba tare da sharadi ba!

KU SAKESHI YANZU KAWAI!

#COVID19

#Freeshaikhzakzaky

Comments

Popular Posts