YAUSHE MUZAHARAR FREE ZAKZAKY YA ZAMA TASHIN HANKALI
Da Sunan Ubangijin da baya Zalunci Kuma Ya Hana Zalinci.
Tsira aminci su kara tabbata ga shugan halitta Annabi Muhammad da yayan gidansa tsarkaka.
Banyi wannan rubutun Dan komaiba saidan na sanar da al'umma Halin da Ake ciki a yanzu.
Sanin kowane cewa Jagoranmu na cikin wani yanayi na Neman taimako da kuma yanci.
Wadda Wasu sunyi yunkurin motsawa domin nemawa jagora yanci amma sai ya zama Da'irarsu ta kirasu da yan tashin hankali.
Wadda mun kasa gane menene tashin hankalin anan.
Muzahararce tashin hankali?
Wadanda sukayi muzahararne yan tashin hankali?
Ko wadda akayi dan shi shine tashin hankali?
To mudai hadafinmu Neman yardar Allah to kowane hali kuma zamuyi iya abinda mukaga zamu iya wajen ganin Jagoranmu ya samu yanci.
In yaso a kiramu da komaima amma dai Muzahara ba Fashi.
Allah Ya Gaggauta Kwato mana Jagoranmu.
Free Free Zakzaky!!!
Comments
Post a Comment