KUNA DA YAKININ BUHARI ZAI GAMA DA MALAM ZAKZAKY(H) DA DA'AWARSA SHI YASA KUKA YI TA MANA SHARRI DA MUNAFURCI........

Ko Kuna so ko ba kwa so wallahi summa Tallahi Almajiran Malam Zakzaky(H) al'umma ce a cikin Wannan al'ummar ta Nigeria..
Ba daga sama muka fado ba,ba tsirowa muka Yi ko ruwa ne ya kawo mu ba...
Sannan a cikin Wannan al'ummar muka taso muka yi wasan kasa,muka Yi karatun allo,Boko da sauran abubuwan da ake yi na yarinta zuwa girma..
Tare daku muka Yi makarantun kwana ko na jeka ka dawo,tare daku muka Yi manyan makarantu University ne, College of education ne, polytechnic da sauran makarantun gaba da secondary Kun San mu mun sanku...
Amma abin mamaki da takaici wai kune kuke rubuce-rubuce da maganganun rashin adalci da rashin tsoron Allahu Ta'ala akanmu...
Abin mamaki ne ace sama da shekaru arba'in da Malam Zakzaky(H) ya kwashe Yana da'awarsa baku gane mu batattu ne wadanda suka cancanta a kashe,a Kona,a binne a daure ba sai da Buhari, Buratai da El-rufa'i suka ce mun cancanci kisa....
Kun ji kunya wallahi, fitowar ku fili da nuna Mana kiyayya da fatan a gama damu da Sanya wakokin yabo da jinjina ga wadanda suka kashe a wani lokaci ya tabbatar da wauta da rashin hankali da tunanin ku...
Duk kisan da aka Mana ba a kashe Mutane dubu dari ba,ba a rushe mana gidaje da makarantu dari ba,bamu daina Muzaharar Mauludi da Ashura ba,bamu daina gudanar da dukkan programs dinmu ba...
Hatta wadanda Sojojin Nigeria da 'Yansanda suka Kama Kotuna dabam-dabam sun sallame su,shi kansa Malam Zakzaky(H) Kotun Tarayyar Nigeria tace an zalunce shi,to yanzu me ya rage muku na kiyayya a garemu.?
Yanzu da yawanku ba kwa kaunar mu hada Ido ko mu hadu daku ko menene dalili...???

Comments

Popular Posts