CoronaVirus A Kurkukun Kaduna?



Rahotonni sun tabbatar da cewa har a ranar Alhamis din makon jiya, bayan bullar cutar CoronaVirus a Nijeriya, an cigaba da kai sababbin mutane da nufin a tsare su a Kurkukun Kaduna inda a nan gwamnatin Buhari ke tsare da Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah.

Duk hakan bai daga hankalin wadanda ake tsare da su a Kurkukun ba, sai a yau da suka wayi gari wata daurarriya da ake tsare da ita a bangaren mata tana tari da zazzabi mai zafi, wanda ake zargin cewa alamu ne na cutar COVID-19 da ake fama da ita.

Wata majiya ta shaida mana cewa, bayan dauke wannan mara lafiyar, an kai ta asibiti inda aka bata magani tare da kokarin yi mata gwajin cutar ta CoronaVirus, wanda sai bayan kwanaki biyu a kan samu sakamakonsa. Sai dai su mutanen da ake daure da su a Kurkukun hankalinsu ya tashi da ganin wannan inda suka ce ba su aminta da zama a irin wannan halin ba.

Daurarrun da ke Kurkukun sun ba da dalilai ga ma'aikatan gidan, daga ciki akwai cewa, tunda ana tsare ne da su ne a waje guda, kuma sauran mutane a cikin gari ma an killace su a gida ba sa fita, to ya kamata ace su ma a dena kawo musu baki cikinsu a daidai wannan yanayin da ake ciki. Saboda ba a san 'status' din lafiyar wadanda za a kawo din ba.

Sannan suka ce, kuma dole ne su ma ma'aikatan Kurkukun su zauna a cikin gidan Kurkukun ba tare da fita ko zuwa gidajensu suna dawowa ba, tunda kowa a killace yake a gari saboda gudun kamuwa da cutar CoronaVirus, ba za su aminta da ya zama ma'aikatan na fita waje su je gidajensu da wasu wurare, kuma su dawo gidan kurkukun su rika mu'amala da su ba.

Wadannan dalilan da aka ki kulawa da su, ya sa mazauna gidan yarin suka fara yekuwar cewa ba su aminta ba a sake su ko a kare su. Nan abu ya rincabe aka fara doke-doke tsakanin wadanda ake tsare da su da masu kula da tsare su din na gidan yari. Nan take aka turo sojoji inda suka rika harbe-harbe a harabar gidan yarin da sunan wai ana yunkurin yin bore a gidan.

Ya zuwa yanzu, shedun gani da ido sun tabbatar da cewa yanayin ya lafa. Sai dai bangaren 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na bayyana fargaba akan yanayin tare da rashin aminci akan cewa ba ana son yin amfani da cutar CoronaVirus bane don cika birin gwamnati na kashe Jagoran Harkar Musulunci da ake tsare da shi da matarsa fiye da shekaru hudu da suka gabata tun bayan yunkurin kashe shi da ya ci tura wanda sojoji suka yi a shekarar 2015.

Mutane da dama suna da ra'ayin cewa ya kamata a gaggauta rage cinkoson wadanda ake tsare da su a gidajen yarin Nijeriya, ko da kuwa ta hanyar shirya zaman kotu a gidajen yarin ne a ba da beli ga wadanda suka cancanta su je su killace kansu daga wannan annoba mai yaduwa.

An kirayi 'yan uwa Musulmi kan su sanya Shaikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah a addu'a, kasancewar ana tsare da su cikin matsanancin halin rashin lafiya a tsawon shekaru ba cikin takura da tsanani. Allah Ya gaggauta kubutarsu daga hannun azzalumai, Ya kuma dauka musu fansa akan masu zaluntarsu da yi musu kama-karya


— Saifullahi M. Kabir 

Comments

Popular Posts