ALLAHU TA'ALA YA KARE TALAKAWAN NIGERIA DAGA CORONA VIRUS MIYAGUN SHUGABANNI DA MUGUNTAR JAMI'AN TSARON NIGERIA


Cutar da bata da border, cutar da bata ware Mai kudi da talaka,bata bambanta malami da jahili,bata bambanta Shugabanni da wadanda ake shugabanta,babu ruwanta da Addini,kabila,yanki,kasa ko nahiya...
Bullar Wannan muguwar cutar ta Sanya wadansu kasashen an samu kusantar juna a tsakanin talakawa da Shugabanninsu, kasashe da yawan gaske talakawansu sun San sun zabi wadanda ba zasu yi kasa a gwiwa wurin taimaka musu da ceto rayuwarsu ba Koda zasu rasa nasu...
Talakawan kasashe da daman gaske suna alfahari da Shugabannin da suka zaba,suna Kuma alfahari da cewa basu Yi zabe a banza ba....
Talakawan kasashe da daman gaske wadanda Wannan muguwar cutar ta shiga sun ga tausayi,jinkai da taimakon gaske daga Shugabanninsu, Likitocinsu da jami'an tsaron kasashensu...
Shin irin Wannan taimakon, tausayin da jinkan zamu same shi daga Shugabannin Nigeria da jami'an tsaron Nigeria.?
Allahu Ta'ala ya Kare al'ummar Nigeria daga Wannan muguwar cutar,ya kawo Mana dauki alfarmar Annabi Muhammadu(S) da Ahlulbaitinsa(AS)...

Comments

Popular Posts