SAMA DA SHEKARU 40 MALAM ZAKZAKY(H) YANA GWAGWARMAYA BAI GAJI DA 'YAN-UWA BA SAI KAI..
Shi kadai ya fara gwagwarmaya,shi kadai ya San Ina aka dosa,shi kadai ya San daga Ina aka tashi,Ina Kuma za a je...
Malam Zakzaky(H) Yana da yakinin abinda yake yi,bai taba shakkar abinda yake yi ba, sannan Yana da Imanin Allahu Ta'ala zai cika Masa burinsa na tabbatar addini a kusa ko a nesa...
Malam Zakzaky(H) ya San dukkan Wanda ya dauki tafarkin Annabi Muhammadu(S), Ahlulbaitinsa da mujaddadai dole sai ya Sha wahala kamar yadda suka Sha...
Dukkan jagororin addini sukan Yi fama da azzalumai,munafukai da mahassada,amma Wannan bai taba kashe musu gwiwar cigaba da gwagwarmaya ba..
Azzalumai da munafukai suna yin dukkan Mai yiwuwa domin ganin bayan jagoran Addini shi Kuma kullum burinsa da fatansa shine su shiriya su zamo Mutanen kwarai su gamu da Allahu Ta'ala a matsayin masu neman uzuri...
Daga fara da'awar Malam Zakzaky(H) zuwa yanzu azzalumai da munafukai sun yi yunkurin hallaka shi,ko su nuna abinda yake ba daidai bane amma Wannan bai taba kawo Masa cikas a tafiyarsa ba...
Ina rokon Allahu Ta'ala ya bamu hakuri, juriya,kawar da Kai da Kuma kyautata zato wa juna da fatan alheri ga kowa kamar yadda Malam Zakzaky(H) yake fama damu....
Comments
Post a Comment