Sakon Ofis Din Sayyid Zakzaky (H) Dangane Da Coronavirus
1. Lalle annobar Coronavirus da ke barazana ga kasashen duniya gaskiya ce. A na kan samun yawaitar mace-mace a kasashe irin su Italiya, Sin (China), Iran da wasu kasashen yamma. Nijeriya kuwa, duba ga irin yanda harkar kiwon lafiya ta tabarbare, to lamarin zai iya yin tsanani fiye da sauran kasashe idan ba an dauki matakin da ya dace ba.
2. Duba ga cewa, mafiya yawan 'yan Nijeriya talakawa ne da ba za su iya daukar matakin zama a gida, ba fita ba na tsawon lokaci, saboda kusan kullum sai an fita ne a ke samun abunda za a ci, kenan babban matakin da mutane za su iya dauka wurin dakile yaduwar cutar shi ne ta hanyar bin shawarwarin masana harkar lafiya ta hanyar gujewa taron mutane da kuma kauracewa cudanyar jiki-da-jiki ta kowace irin hanya.
3. Akwai bukatar kula sosai yanzu tare da daukar mataki. Yanzu ba lokacin yada maganganun an-yi an-ce ko zarge-zarge kan cutar ba ne, domin yin hakan zai iya hana daukar matakan da ya kamata a dauka na dakile yaduwar cutar.
4. Muna mika sakon ta'aziyya ga Iyalan da suka rasa 'yan uwan su sakamakon wannan annobar.
Allah Ya yi mana tsari daga wannan annobar.
Daga: Shafin Twitter na office din Sheikh Zakzaky da ke Masshad: @SZakzakyOffice
25/03/2020
Comments
Post a Comment