KA SAUKE HAKKIN SHUHADA KUWA?
Assalam yan uwa kamar yanda muka sani ne cewa taron Yaumu Shuhada ya zo Wanda insha Allah za a gabatar yau Asabar 21/March/2020 a garin Abuja, sai dai kuma gaskiyar lamari yan uwa sun gaza sosai wajen sauke wannan hakkin da ya rataya a wuyansu (Hakkin Shahada). Kamar yanda muka sani shi fa wannan ba Infaqi bane, Hakki ne da ya zama wajibi akan duk wani wanda ya amsa sunansa a matsayin Almajirin Sheikh Zakzaky (H) ya biya, ba wai infaki bane.
Wannan Hakki din Naira 100 ne a duk wata wanda ya kamata ace duk yan uwa sun sauke duba da irin yanayi na waki'o'i da ake fuskanta tun daga shekarar 2015 (Ranar da Azzaluman Gwamnatin Nijeriya ta afka mana a Zaria) har zuwa yanzu muna cikin waki'a ne kuma kullum masu rauninmu ana kashe musu kudi ne.
Kamata yayi ace yan uwa sun kara akan abin da suke bayarwa ma, amma sai ya zamana cewa ba a sauke hakkin ma bare har a kara. A koda yaushe kuma 'ya'yan Shahidanmu da Yan uwanmu da Azzalumai suka Raunata a taruka daban-daban suna bukatar magana da kulawa, ba wani bane zai zo yayi mana wannan aikin, mu din ne dai!!
Ana kira ga yan uwa duk wanda Allah ya bashi ikon zuwa taron ya tafi da NASA hakkin wanda kuma bazai samu daman zuwa ba yana iya bada sako ga masu zuwa ko wakilin Shuhada na yankinsu. Muna fatan Allah ya bamu ikon sauke Hakki na wadannan Shahidan namu, domin sun tafi a tafarkin Allah kuma sun bar mana amanan 'ya'yansu.
- 21/March/2020
👇👇👇
https://ansarulmahdi.blogspot.com/
Comments
Post a Comment