SHAIKH ZAKZAKY (H) NE GATAN WANNAN AL'UMMA
Da ba dan wannan bawan Allah ba, da Allah (T) kadai ya san halinda wannan al'umma za ta kara tsunduma a ciki, dan a gaskiya mutum na iya cewa babu fata sam. Wannan bawan Allah arzikinsa kowa yake ci a kasar nan, sakamakom da'awarsa ne wasu manufofi na zalunci daga makiya suke rushewa, jin tsoron akwai wani bawan Allah da yake da'awar abi Allah shiyasa makiya ko sun tsaro tsarinsu tsarin yake samun nakasu.
Wajibin wanda ya gane ne, ya yi aiki dare da rana domin taimakon wannan kira, ta yadda idan ya tabbata ya'ya da jikoki da tattaba kunne da unhuhu za su ji dadi, su sa ma iyayensu albarka. Wanda yaji sautin wannan kira wajibinsa ne ya bayarda gudumuwa,
Shaikh Zakzaky (H) duk da hali da yanayi da suke ciki basu fitarda fatansu akan cewa nasara na nan tafe ba kurkusa, mu da muke walwala yaushe za mu fitarda fata alhalin Allah (T) ya samar mana jaruminda baima zalunci saranda ko kadan? Allah (T) ya yi mana taimako.
Comments
Post a Comment