YAUMUS-SHUHADAH 2020:. DUKKAN WADANDA KUKA KASHE MANA BABU DAYA DA MUKA MANTA BALLANTANA MU YAFE..
Jagoran Harkah Islamiyya Malam Zakzaky(H) lallai ya San tabbas azzalumai da karnukansu ba zasu taba kyale da'awarsa ba, Wannan ne yasa ya assasa Wannan mu'assasar mai suna Mu'assasatus-Shuhada domin kula da iyaye,Iyalai da 'ya'yan wadanda azzalumai suka kashe a Wannan Harkah....
Harkah Islamiyya karkashin jagorancin Malam Zakzaky(H) tana sane da wadanda suka kashe Muhammed Bello shahidin farko a harkannan,tana sane da wadanda suka kashe Abubakar Shehu Modomawa,tana sane da dukkan wadanda suka kashe Mata 'ya'ya da wadanda suka bada umurnin kisan, Shugaban kasa ne,Gwamna ne, Sarkin gargajiya ne, Sojoji ne, 'Yansanda ne, 'Yan banga ne, 'yan-iskan gari ne ko ma wanene...
Yadda muke taskace tarihin dukkan wadanda suka kashe Mana 'yan-uwa haka nan muke taskace rawar da kowa ya taka a kashe Mana 'yan-uwa haka siddan..
Yadda ba zamu manta da wadanda azzalumai suka kashe Mana ba,haka Nan ba zamu manta da wadanda suka kashe su ba..
Yadda wadanda aka kashe Mana suka dake akan abinda aka kashe su akai haka zamu dake akai babu gudu babu ja da baya...
Sannan muna musu alkawarin ba zamu daina ba kuma wallahi summa Tallahi sai mun dauka musu fansa anan kusa ko nesa insha Allahu Ta'ala.....
Comments
Post a Comment