TUNATAR DA KAI KAN AL’AMARIN JAGORA H
(6)
Wasu suna cewa me nake nufi da duk dogayen rubutun nan da nake yi? Ina cewa, ina tunatar da mu baki daya ne, cewa Harka Islamiyya tafarki ne na gwagwarmaya da zalunci da azzalumai. Kuma jagoran Harkar nan yana nufin hakan ne a furuci da aikinsa. Don haka ya kamata mu yi wa kanmu tunani mu gane cewa shin mun fahimci abin da ke wuyayenmu kuwa?
Misali, Jagoranmu (H) ya taba cewa: “Inda da gaske ne akwai wasu mutane wai sunansu Boko Haram, sun sace wasu ‘yan mata (na Chibok), da da gaske ne, wallahi da mun kwato su.” Mun tina wannan maganar? Ya Mukai ‘reaction’ a lokacin ma? Kabbara muka kwada ko? Kowannenmu nake tambaya; Shin mun taba zama musamman mun yi nazarin wannan maganar da akai mata rantsuwa? Cewa me Jagora ke nufi? In da gaske din ne su waye za su kwato su din, ta yaya kuma? Ko muna ganin da ace da gaske din ne shikenan Jagora ba ma zai fara fadan hakan bane?
Musamman bangaren samar da tsaro da nizamin Harkar Musulunci, yaushe muka taba yin taron nazarin maganar Jagora ire-iren wadannan, mu fahimci me yake nufi, muka kuma fara shirin samar da yanayin da in na gaske din ya zo za mu cika ‘hope’ din da Jagora ke da shi a kanmu da ya sa yake iya bugan kirji ya yi bayani haka?
Ashe ba mu ji ya fada Ko da yake gwamnati ke bayan garkuwa da mutane a yanzu, amma da ya zama abin ya ci tura yai Kamari, mun taba zama musamman muka yi nazarin cewa, Jagoranmu (H) ya fadi a Yaumus Shuhada'u 2014 cewa: "Wannan abin da ke fuskantomu a Kasar nan (na kashe-kashe da zaluntar al'umma) ya shafe mu kai tsaye, kuma fuskantarsa da duk irin abin da muke iyawa, aiki ne ga addinin Musulunci, kuma duk wanda aka kashe a cikinmu (a kan wannan) Shahidi ne" ba? Mun tuna hakan? In ba Jagoranmu shikenan komai ya daidaice kenan sai dai mu rika cewa Amawa, duk abin da ke faruwa sakamakon taba Jagoranmu ne, Allah ya kara? Shine alkiblar Gwagwarmayar Musulunci kan lamarin? Wane abu muka yi na kokarin cika zancen Jagoran al'umma (H)?
Abin da nake cewa shine, su mutanen nan sun kama Jagoranmu ne sun kulle bayan da suka nufi kashe shi Allah ya raya shi, saboda su kautar da mu daga hadafin Jagora din na kokarin samar da yanayin da zai yi Muqawama, ya yi gwagwarmaya, ko fada da zaluncin nizamin zalunci a kasar nan. Sai suke ganin a sadda suka kama shi, shikenan za mu gaji har mu koma kawai muna yin taruka irin yadda ‘yan Shi’ar kasuwa ke yi, muna cewa Yazidu tsinanne, muna cewa ana zalunci amma saboda an taba mu ne ake yin zaluncin ma, sai ya zama wadanda muke kira Amawa sun dena fahimtarmu, sun cire fata daga gare mu, bare ai batun wai wata rana za mu yunkura mu kwata musu yanci su mara mana baya.
Mafitarmu kwara daya ce, ita ce gwagwarmaya a tafarkin Allah, wanda kai tsaye shine tashi a yi duk wani abu da zai dakile azzalumi daga zaluncinsa a kan Jagora da kan al’umma baki daya, wanda in da ace sun ga cewa ko ba Jagora ba zai yiwu su mike kafa su yi zalunci yadda suke so ba, za mu taka musu burki kamar shi, da za su ga ba su da bukatar kawar da shi kadai, ko cigaba da tsare shi. Amma in aka wayi gari suka ji muryarsa ce kawai da ta wanzu ke fada da zalunci, aikinsa ne kawai sadda yake waje ke nuna cewa Harkar Musulunci motsi ne na neman yanci da kawar da zalunci da shimfida adalci, to tabbas za su gane sun yi galaba, kuma ba za su sassauto ba. Za ma su ga cewa kawar da shi ne kadai mafitarsu.
A yayin da nake karkare wannan rubutun nawa, ina mai kira garemu baki daya, da mu zauna mu yi nazari manya da kanananmu, kar mu ce kanmu ya kulle mun rasa abin yi, abin yi kwara daya ne, shine fitowa kwanmu da kwarkwata a ko da yaushe ba tare da mun nuna gazawa ko gajiyawa ba, muna masu kira a saki Jagoranmu. Idan har mai zalunci bai saurara na kwana daya ba, wanda ake zalunta ko mai kokarin kawar da zalunci bai ga ta hutu ba.
Ya wajabta ga ‘yan uwan da Allah Ya hore musu miliyoyi da dubban daruruwan kudade suke juyawa, suke sayan gidaje da filaye da kayayyaki, suke kara aurarraki da dinka sabbin shaddoji da yi wa wadanda suka ga dama kyaututtukan bajinta, su gane cewa dukiyar Allah Ya ara musu ne don su yi aiki wa addininSa, kuma a cikin hidimtawa addinin ne albarkar Dukiyarsu duniya da lahira yake, a cikin yi masa rowa ko tsakura masa wani abu cikin dacin rai ko cikin neman yabo ba kawai akwai asara ne ga dukiyar ba, akwai saraya da tabewa ne a gare su.
Ahlud-Dusur (Yan kasuwa da Manoma), Resoureces Forum (Ma’aikata), da sauran ‘yan uwa baki daya na Harkar Musulunci mu wa Allah mu samar da yanayin da zai zama mun kawar da tsoron wasu abubuwan da kudi ke yi wajen fafutukar kiran a saki Jagoranmu wanda shine dalilin shiriya kuma silan tsirarmu a wajen Allah (T).
Abin kunya ne sosai ya zama akwai masu gina gidajen miliyoyin kudi, suna da kantina da masana’antu da shaguna suna juya kudi, amma ai waki’a a ji wa ‘yan uwa 10 rauni ace an gaza samun mai ba da Miliyan daya a kula da maganinsu har sai sun galabaita ana neman tallafi kana bada naira dubu 20 ko 50. Ba ka fahimci cewa kai Harkar naka na iya zama ba da wannan infakin bane, wasu su wakilce ka a ba da lokaci, jiki da rai kamar yadda ka wakilce su a dukiya? Kar aji ina ta maganar masu miliyoyi, shi mai Infaki mai Infaki ne ko da Naira daruruwa yake da shi. Kuma Allah Ya san kowa.
Ya ‘yan uwa masu girma, mu dena bawa kanmu uzirori, Muzaharori za mu tsayu da su kamar yadda muka faro a farkon waki’a da yawanmu na adadi da ruhin Imani da Kankan da kai ga Allah (T) har ya zama mun samar da yanayin da al’amarinmu zai zama labaran duniya, wannan hanyar ya fi komai saukin kusanta mu da nasarar Allah (T).
Al’amarin Muzaharar Abuja da ta Kaduna, abu ne da ya fi kowane abu muhimmanci mu karfafe shi, in aka wayi gari dukkanmu mun fahimci cewa da motsi ne makiya za su gane cewa ba su yi galaba a kanmu ba, to ya kamata duk mu kasance tare da masu motsin a aikace da gangunan jikkunanmu gwargwadon hali, da kuma dukiyarmu musamman ga wanda har a wajen Allah ya tabbatar cewa yana da uzurin da ba zai iya kai samuwarsa wajen Muzaharar ba.
Mu yi abin da har a gaban Allah (T) za mu iya tsayawa mu da Shi, muce masa Ya Ubangijinmu, mun tashi mun tsaya kyam don kokarin adalci ya tabbata kan al’amarin bawanKa, duk da makiya basu gushe ba suna zaluntarmu, ba mu gushe ba muma har sai da muka samu nasarar cimma manufar tsayuwar tamu, ta hanyar kubutarsa ko ta hanyar riskar kyakkyawar rabo (Shahada). Namu mu sauke wazifar da ke kanmu, Natija kuma na wajen Allah (T) ne.
Ina neman yafiyar duk wanda na bata masa rai. Ina kuma rokon afuwar duk wanda bai fahimceni a wata gaΙa ba. Kamar yadda nace, tunatarwa ce kawai, in aka samu kashi 1 cikin 100 na daidai a cikinta, ina fatan mu hadu mu yi aiki da ita. Allah Ya ji tausayinmu, ya bamu ikon tsayuwa a tafarkinSa.
18/2/2020.
Pleaseπ Share linkπππ
https://ansarulmahdi.blogspot.com/

Comments
Post a Comment