*ALLAH SARKI MATA*
.
.
Zata zauna a gida ta nutsu da kyawawan Dabi'unta tana jiran Allah ya kawo mata Mutum nagari,
Kwatsam Sai wani yazo mata da kalamai da dadin baki ta yarda dashi sai ya 'bata mata lokaci ko ya bata mata rayuwa
Sannan ya Gudu ya barta cikin Qangin yaudara mutane kuma suce  *''TAKI AURE''*
.
Idan ta fara kasuwanci don ta samu abinda zata tsira da mutuncinta si kaji ana cewa ai '' *'YAR ISKA CE''*
.
Idan kuma ta koma makaranta domin ta samu rayuwa mai inganci sai kaji mutane sunce *'' BAZAMU AURETA BA 'YAR DUNIYA CE sannan  BAZAKA IYA JUYATA BA''*
.
 Wacce ta samu tayi Auren kuma Idan aka samu rashin sa'a Mijin yai ta Gallaza mata karshe ya dirka mata saki, Bayan kuma ta gama mika wuya tayi amanna dashi kawai hakan sai kaga mutane  sun rufe idanu sunce *''TAQI ZAMAN AURE''*
.
Tambaya agareku MAZA
.
*''TAQI AURE''* To wayaki Auren nata..?
.
*YAR ISKACE* to waye abokin Iskancin nata..?
.
*YAR DUNIYACE*  to dawa take duniyancin..?
.
*TAKI ZAMAN AURE* to waya sakota..?
.
Don haka maza muji tsoran Allah
.
Kar ka yaudari Diyar wani
Kar ka bata Diyar wani
Kar ka aibanta Diyar wani
Kar ka wulakanta Diyar wani ala bashshi ko kaima naka sa tsira da mutunci
Mu tunafa Allah zai tambayemu akan hakan
Sannan kaimafa zaka haihu
Bafa zaka so aiwa 'ya 'yanka hakaba ko 'yan uwankaba
.
Maza muji tsoran Allah
mu dinga tausayawa Mata
mu dubi gajartacciyar rayuwarsu

✍️ Young Ahmad Snk


Comments

Popular Posts