BABU ABINDA NAKE GANI A FUSKAR BUHARI SAI JINANEN DARURUWAN ALMAJIRAN MALAM ZAKZAKY(H) DA YA SHEKAR A ZARIA..
Wannan tsohon Wanda ya kwashe Shekaru sama da saba'in a Duniya amma zuciyarsa cike take da mugunta da rashin tausayi,abin takaici ne gaskiya.
Idan na kalli fuskar Buhari babu abinda Yake zuwa a zuciyata sai la'anta da neman Allahu Ta'ala Ya gaggauta daukar mana fansa akan wannan azzalumin Wanda bai taba amfana mini komai a rayuwa ta kamar yadda Dakta Mustafa Sa'id ya amfana mini ba.
Me zance ko me kake tsammanin zan ce idan na kalli fuskar mugun tsohon da ya shiga tsakani na da Sheikh Turi.? Ya raba ni da Sheikh Mukhtari Sahabi.? Sheikh Mustafa Lawan Na-Sidi da Sheikh Kabiru Alkanawiy.?
Kana tsammanin zan yi addu'a da fatan alheri ga Wanda yasa aka kashe Mata da Yara marasa makami haka siddan.?
Da umurnin Buhari aka kashe'ya'yan Malam Zakzaky(H) uku,aka rusa gidan Malam Zakzaky(H), Makaranta da wurin da aka binne Mahaifiyar Malam Zakzaky(H), wannan ta'addancin ne zai sa na kaunaci Buhari ko na so shi.?
Kaunar Buhari ba ta cikin shikashikan Musulunci,ba ta cikin dokokin Nigeria,ba ta cikin ka'idojin rayuwa,don haka kiyayya da fatan Allahu Ta'ala Ya gaggauta daukar mana fansa akan Buhari wata wazifa ce Mai girman gaske a gareni.
Idan Buhari Yana da Wuta ya gaggauta jefani cikinta,idan Kuma Yana da aljanna kada ya saka ni a cikin ta Koda na Yi aikin da Yake so.
Share linkπππ
https://ansarulmahdi.blogspot.com/
Comments
Post a Comment