Daga Littafin HARKAR MUSULUNCI Na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H):

Harkar Musulunci bata da ‘Headquter’ na gini (property), amma batun link (alaka) da waje, ai mu muna ganin mu bangaren ‘Global Islamic Movement’ ne. Mu bangaren Harkar Musulunci na Duniya ne.

Shi Movement din (Harkar Musulunci) kamar yadda nace ‘Concept’ ne, ba ‘Organization’ ba. Ba Kungiya bace. ‘Concept’ ne, wanda duk yake da wannan ‘idea’ din ‘automatically’ shi dan ‘Movement’ din ne. Don haka duk inda Movement take, bangare ce na Islamic Movement din duniya.

Na’am, muna koyo daga ‘experience’ din wasu. Kaga a Iran ai ‘Islamic Movement’ ne ta yi nasarar ‘revolution’ ta kafa gwamnati ko? To, kaga a Lebanon kuma ana ta fafatawa da ‘Movement’ din. Hizbullah da yake su suna yaki ne sosai da makami. Muna iya cewa su Hizbullah ‘Military wing’ ne na Islamic Movement a Lebanon. Hizbullah ba ita a kan kanta ne Movement din ba, kamar Harisawa ne, su ‘military wing’ ne na Islamic Movement a Lebanon.

Ko ina (a duniya) akwai Islamic Movement, sai dai matakin wani wajen yana da karfi, wani wajen kuma madaidaci ne, wani wajen kuma yanzu ne yake dagowa.

Amma kamar yadda na fada, a nan da muke a Nijeriya, makwaftanmu, wadanda suke bangarenmu ne bamu dauka su sun fito daga wata kasa bace ta daban. Kamar misali ‘yan Niger, muna Harka guda ne. Ba muna cewa ‘Islamic Movement’ na Niger bane. Shi wannan Islamic Movement din shine kuma har ila yau ya yadu akwai shi a cikin Niger. Kuma ma dai a wajenmu da mu da Niger komai namu daya ne, tarihinmu, asalinmu da komai da komai....

...Hanya guda daya muke da ita (na samun kudade a Harkar Musulunci), kuma ita kenan dai har yanzu, bamu da ta biyu. Shine kawai mutane su tattara gudummawa. Su mutanen da suke Harkar, su suke tattara kudade.

Daga waje kam bamu samun gudummawar kudi, sai dai na ‘experience’ tunda ana gogayya da ‘yan kasashen waje, za ka koya daga kwarewan wasu, su ma za su iya koya daga naka. Ko da yake muhalli na iya bambanta. Wasu abubuwan da za mu iya aikatawa a nan, ba za a iya yinsu a wasu wurare ba. Kowace ‘society’ ta bambanta, kowa zai dubi yadda muhallin da yake yake ne.

Kaga a wasu ‘societies’ kamar Lebanon, su suna samun masu kudi ya zama sun ba Hizbullah abubuwa, kamar dogayen gine-gine su yi asibiti, ko makaranta. A Lebanon, masu kudi, miloniyoyi suna basu gudummawa na miliyoyin kudade, amma mu a nan masu kudin (kasar) basu bamu ko kabo, 'yan Harkar ne ke tara kudadensu.

Comments

Popular Posts