MAGANIN KOWACCE ANNOBA DA KONNE BALA'I IDAN YA SAUKA
Ayatullahi As-Sheikh Bakir Sharif Al-Qurashi yana cewa: Ayatullahil Uzmah As-Sayyid Muhsin Al-Hakim (Q.S) ya tura wani daga cikin Daliban Ilimi a Kasuwar Shuyukh domin yayi Tabligi. A lokacin da Dalibin ya fara aikin sa na Tablig sai Annoba ta rutsa Garin, ta bi gida gida tana gamawa da Mutane, sai Shehin Malamin ya nemi Kariya a wajen Imamu Husain (as), a cikin Bacci kuwa sai ya ga Imamu Husain (as), sai Imam (a yace da shi: Ka tsorata ne ko Ya Sheikh!? Sai yace Na'am. Sai Imam (as) yace da shi: "Ka rubuta wannan a kofar Gidanka, sannan Ka umarci Shi'a su ma su rubuta shi....".
Sai Shehin ya farka ya rubuta shi ya kuma umarci Shi'a da su Rubuta shi. Duk gidan da rubutun yake kuwa Annobar ba ta shige shi ba.
Kuma As-Sheikhul Qurashi yace: A lokacin Yaqi Iraqi ba wani soja da muka ba wa ya rubuta shi face ya dawo ga Iyalansa Lafiya.
Ga Hirzin da Imamu Husain (as) ya sanar da As-Sheikh din a cikin Mafarki:-
"إني اريد أماناً يابن فاطمة مستمسكاً بيدي من طارق الزمــن....
من فاطم وبنيها ثم والـدها والمرتضى حيدرٌ أعني ابا الحسن"
Ana rubuta Hirzin ne a Kofar Gida daga ciki.
Allah ya kare dukan Al'ummar Annabi daga kowacce Musiba.
Comments
Post a Comment