MUSULUNCI NAN SAI YA MAMAYE DUNIYA?
MUSULUNCIN NAN SAI YA MAMAYE DUNIYA
To, Musuluncin nan, ko kun ki ko kun so, mun san ma dai kun ki din, amma Musuluncin nan Allah ya yarda dagowa zai yi. Kuma sai ya mamaye duniya.
Wannan Manzo (S), sakonsa da aka murguda, sai al'umma ta fahimci meye sakon, waye hakikanin wannan Manzon, kuma me ya yi kira ya zuwa gare shi. Wannan Manzon shi ne wanda ya yi nasara a kan makiyansa ba tare da ya yi sara da Takobi ba.
Makiyansa su suka je suka kai Takobi. In har ya kare kansa a matsayin kare kai ne, sai ga shi ya fi karfinsu, ya shiga Makkah da adadin da ba za su iya yaka ba. Suka fito suka dora hannuwansu a keyukansu, suna tsammanin duk fille musu wuya zai yi. Ya ce da Su me kuke tsammanin zanyi muku? Suka ce; ai kai dan dangi ne, kai mutum ne mai tausayi. Yace; ku tafi, an yafe muku, an sake ku; ku sakakku ne.
–Sheikh Zakzaky (H)

Comments
Post a Comment