Hatsaniya a gidan yarin Kaduna inda ake tsare da El-Zakzaky



Sheikh El-zakzaky na tsare a hannun gwamnati tun 2015

Wasu fursunoni da ke babban gidan yarin Kaduna sun tayar da yamutsi inda suka bukaci gwamnati ta sake su saboda fargabar kamuwa da coronavirus.

Rahotanni dai sun ce an yi yamutsin ne bayan wasu fursunoni sun nemi a sake su suna masu ikirarin cewa wasu fursuna biyu sun mutu sakamakon coronavirus.

Sai dai shugaban gidan yarin Sanusi Mu'azu Dan-Musa, ya shaida wa BBC cewa batun mutuwar fursunonin ba gaskiya ba ne.

A babban gidan yarin na Kaduna ake tsare da shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta Islamic Movement in Nigeria Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa.

Rahotannin sun ce 'yan sanda sun rika harbi a iska da kuma rufe hanyoyin shiga gidan yarin domin hana fursunonin tserewa.

Hakan ya sa kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi, a sanarwar da kakakinta Ibrahim Musa ya aike wa manema labarai ta yi kira ga dukkan hukumomin da ke da hannu a daure Sheikh Zakzaky su tabbatar da tsaron lafiyar malamin da matarsa.

"Za mu dora alhakin kan gwamnatin tarayya idan wani abu ya faru a kansu. Nauyin kare lafiyar dukkan fursunoni a gidan yari, musamman a lokacin annobar COVID-19da ta addabi duniya, yana kanta, kasancewar doka ta ce kowa ba shi da laifi har sai kotu ce ta tabbatar da hakan," in ji Ibrahim Musa.

Amma Sanusi Dan-Musa, ya ce malamin da mai dakinsa ba sa fuskantar wata matsala.

"Bangarensa daban...Yanzu haka daga wurinsa nake baccinsa yake yi," in ji shugaban gidan yarin.

Kasashe da dama dai sun saki fursunoni saboda fargabar kamuwa da coronavirus.

A ranar Litinin, hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun saki shugaban 'yan hamayyar kasar, Hama Amadou, bayan da shugaban kasar ya yi masa afuwa a daidai lokacin da coronavirus ke ci gaba da yaduwa a kasar.

— BBC Hausa.

Comments

Popular Posts