*SHAIKH USMAN DAN FUDIYE, IMAM KHOMAINI, SHAIKH ZAKZAKY (H)

Wadannan bayin Allah da sunan su ya zo a sama, duk abu guda suka kira al'mmarsu akai. Wannan abin kuwa shine kangarewa tsarinda ya sabawa na Allah, da tabbarda tsarinda Allah (T) ya yi umurni abi. A karkashin wannan tsarinne adalci, tausayi, gaskiya, da shiriya suke ciki. Duk da cewa akwai banbancin mazhaba musamman a tsakaninsu da Shehu Usman dan Fudiye , amma manufa da hadafinsu guda daya ne.

Shehu Usman dan Fudiye a tarihin kasar hausa kusan hatta wanda baiyi karatu ba yana da labarinsa da abinda ya yi na jaddada Addini a wannan nahiya tamu, wanda ya zama tun bayan wancan lokacin bayan turawan mulkin mallaka sun zo daga baya sun mallake wannan kasa ta mu, ba a kara samun wani mai da'awa da ta yi kama da ta Shehu ba, sai da Jagoranmu ya zo, sannan aka fahimci kiran Jagoranmu da na sa abu daya ne babu banbanci ko kadan.

Abinda Shehu ya kira al'ummarsa akan ta dawo ya zama ta aikata shi a aikace, shine Imam khumaini (QS) ya kira al'umma akai, kuma har wa yau shine dai Jagoranmu yake kira, irinsa ne kuma bayin Allah suka tsaya kyam a kai, shine kuma A'imma (AS) suka aikata, shine Annabi (S) da sauran Annabawa suka kira al'ummarsu a kowane zamani.

Shi kowane irin zamani yakan zo da irin nasa yanayi da dacewa wajen cancanta a kira al'umma da shi, alal misali yanzu a wannan lokacin ba za a hada shi da irin zamanin da Shehu Usman dan fudiye ya kira jama'arsa da shi ba a wancan zamanin. Yanzu duniya ta zama kauye guda, ta hanya mai sauki mutum zai iya sanarda sakonsa cikin lokaci da yawa aji.

Shi irin wannan aikin da wadannan manyan bayin Allah suke yi, ba fa kololuwar karatu bane ke sa wa ayi shiba. Zabin mai yi din daga Allah yake, shiyasa duk sassake sassakenda za ayi ba za a iya sassake wannan dashen da Allah (T) ne ya dasa shi ba.

Da'awar Imam khumaini itace dai ta Jagoranmu a wannan lokaci, ba su da banbanci ko kadan, shiyasa mabiya suke kishin ruwan shajja'a su da irin tsayuwar Imam da almajiransa a wancan zamanin, da anyi ma mabiya haka shikenan an biya su da abinda suke so tun tuni. Fatanmu Allah (T) ya yi amfani da mu wajen taimakon wannan kiran har karshen rayuwa, Allah (T) ya amfanar da mu.

— 18/03/2020.

Comments

Popular Posts