ABIN DA YA FI DAMUNMU DANGANE DA AL'UMMA:
__Cewar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H)
Cikin Littafin Harkar Musulunci
Kasantuwar su mutane ne da suke gani ba su san mene ne mafita ba, ka san idan mutum yana cikin wani hali, kuma ya san meye mafita, ka ga ya zama da sauki, tunda ya san ta inda zai bi ya fita kenan. Amma mafi yawan mutane sun san akwai matsala. In ka tambayi mutum ko wane irin mutum ne, ko da mutum A'diy' ka tare ka tambaye shi ya san akwai matsala, amma bai san meye mafita ba. Don haka ne ma in suka tashi wani lokaci suna neman su fidda kansu, sai su yi wanda zai dada dilmiya su.
Alal Misali, Wasu shekaru da suka gabata sun yi zabe, sai kuma suka ga sakamakon zaben da aka fitar ba wanda suka zaba bane. Amma da suka tashi sai suka shiga ciccinna wuta a gidajen shugabannin siyasa, wanda ba abin da ya kamata su yi ba kenan. Ka ga mutum ya san da matsala, amma bai san magani ba. Kuma abin takaici ba a shirye yake ya saurari wanda ya sani ya gaya masa ba. Ka ga wannan abin takaici ne, ka ga mutum yana cikin wani dimuwa, ga mafita, amma bai san abin da ya dace ba.
Alal misali, kamar a ce ana cikin wani babban zaure, sai gobara ta tashi, ga kofar da in aka bi za a fita. Amma sai mutane suna ta kaiwa da komawa zuwa inda mai yiwuwa ma konewa za su yi. To wannan shi ne babban abin da ya dame mu. Cewa ga mutane suna cikin wani hali. Amma ba su san mafita ba, kuma kaico. Da ma idan aka fada musu ga mafitar za su yarda. (amma) ina! Za su ga kamar kana nufin ka hallaka su ne.
Comments
Post a Comment