BA MU YARDA DA CI GABA DA TSARE SHAIKH ZAKZAKY BA!
👇
A makon jiya labari ya bazu cewa, wani kokari da aka yi na Likitoci su duba Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky yadda ya kamata a birnin Kaduna ya ci tura, saboda kin amincewar Hukumar gidan yarin Kaduna, inda ake tsare da shi. Wannan ba shi ne karon farko da irin hakan ya faru ba. A karshen watan Disamban bara irin hakan ta faru, wanda ya sabbaba da aka je Kotu a watan Fabrairu, Alkalin kotun ya sa aka kira Shugaban gidan yarin ya shaida masa cewa Shaikh Zakzaky suna da hakkin a bar Likiti ya duba su yadda ya kamata ba tare da kawo wani tarnaki ba.t Abin takaici sai ga shi wannan Shugaban gidan yari bai bi umurnin Kotun ba, yana ta kawo tarnaki kan duba lafiyar Jagoranmu da iyalinsa da suke tsare a gidan yarin tun bara.
Wannan al’amari abin a yi Allah wadai da shi shi ne, a kuma jawo hankalin jama’ar kasar nan da ma duniya baki daya hatsarin da wannan mataki yake da shi ga zaman lafiyar kasar nan. In banda zalunci yaya za a yi a ce Kotu ta ce a bar Jagoranmu ya ga Likitocinsa su yi abin da ya kamata, amma sai wasu jami’an gwamnati su hana? Me hakan ke nufi?
Mun yi amannar cewa gwamnati na da nufin idar da burinta na kashe mana Jagora ne, wanda Allah bai yarje mata ba a kisan kiyashin Zariya na 2015. In ba haka, yaya za a yi kowa ya san bawan Allah da iyalinsa Malama Zeenah ba su da lafiya tun sannan, amma duk wani kokari na sama masu lafiya a waje da cikin gida sai ya gamu da cikas? Muna sane da cewa lokacin da Kotu ta amince a tafi da Shaikh Zakzaky da iyalinsa Indiya don duba lafiyarsa, gwamnati ce ta daburta lamarin, abin da ya tilasta wa Jagoranmu gwammacewa ya dawo gida, da a duba lafiyar tasa a can. Duk da haka gwamnati ba ta daddara ba, kotu ta yarda a nan gida Nijeriyar ma a duba shi, amma suna ta jan kafa kan lamarin.
Baya ga wannan mummunan zaluncin, yanzu haka akwai wasu ’yan’uwa musulmi da suke tsare duk da munanan raunukan da jami’an tsaro suka ji musu a yayin muzaharar Free Zakzaky a Abuja tun kusan watanni bakwai. Gwamnati ta ki yarda a kula da lafiyarsu yadda ya dace. Ga kuma wasu ’yan’uwa musulmi na garin Yawuri da ake tsare da su a kurkukun Birnin Kebbi, alhali ba a wani taro ko muzahara aka kama su ba. Har gida aka bi su aka kama su. Haka kuma ga wasu ‘yan’uwa na Malumfashi da su ma ake tsare da su bisa irin wannan salo. Mafi tsanani ma shi ne bude wuta da harsasai masu rai da jami’an tsaro suke yi a Kaduna in an fito muzaharar Free Zakzaky, inda a kwanakin baya suka ma kashe wani yaro matashi.
Muna so al’ummar kasar nan da ma na kasa da kasa su sani cewa zaluncin nan ya isa haka nan! Komai fa yana da iyaka!! A gaskiya wannan hanya da gwamnati ta dauka ba mai bullewa ba ne. Hakika ba zai haifa wa kasar nan da mai ido ba. In dai ana son zaman lafiyar al’umma, kowace iri ce, dole a tabbatar ba a zaluntar wani bangare na al’ummar. Kuma alal hakika kowa ya san cewa ‘yan’uwa musulmi na Harkar Musulunci mabiya Shaikh Zakzaky wani bangare ne na wannan al’umma ta Nijeriya. Don haka masu mulki su bar ganin suna zaluntar mu, ba abin da ke faruwa, su dauka daidai suke yi, kuma ba abin da zai biyo baya.
Wannan da ma bukatarmu ta tun asali bayan kisan kiyashin Zariya na a saki Jagoranmu Shaikh Zakzaky da sauran wadanda suke tsare, sune suka sake sa wa mu fito kwanmu da kwarkwata muna yekuwar “Free Zakzaky!” Muna ganin ya fa kamata a saurare mu, tun lokaci bai kure ba.
Duk da mun yi amannar cewa Allah ba zai bai wa azzalumai nasara a kan muminai ba komai daren dadewa, duk da haka ba za mu zura ido ana neman kashe mana Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky ba. Mafitar gwamnatin kasar nan shi ne ta bi umurnin kotu na tun shekarar 2016, ta sake shi, ta ma biya shi diyya. Muna nan a kan bakanmu, ba za mu gajiya ba! Muna rokon Allah ya dafa mana a kan wanan buri namu da muka dade mun neman hakkakuwarsa.
Amincin Allah ya tabbata ga wadanda suka bi shiriya.
SA HANNU:
SHAIKH ABDULHAMID BELLO ZARIA
23 GA RAJAB, 1441 (18/03/2020)

Comments
Post a Comment