Shawarwarin masana akan kwayar cutar corona-virus

Idan wanda ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta Corona-virus yayi atishawa mai dauke da kwayar cutar zai yiwu kwayar cutar ta tashi ta hanyar iska bisa tazarar mita uku kafin ta fadi a kasa. Shi yasa ake ta kira ga mutane su guji shiga cinkoso. sannan ka bada tazarar a kalla mita uku tsakaninka da mai tari ko atishawa, idanma baka bada mita ukun ba, ka tabbatar kana sanye 'face mask' mai kare shakar kwayoyin cuta.

Idan kwayar cutar Corona-virus ta fadi a kan wani ma'adani (kamar karfe da dangoginsa) ta kan rayu na tsawon sa'o'i sha biyu shine mafi karanci, don haka idan ka taba wani abu makamancin haka akwai bukatar ka gaggauta wanke hannunka da sabulu, Omo, ko wani 'detergent' wanda ke kashe kwayoyin cuta. shi ya sanya wanke hannun yake da muhimmanci, ta yiwu ka taba inda kwayar cutar ta ke amma baka sani ba, don haka ka guji taba fuskarka da hannunka musanman idanunka, hanci, ko baki, kar ka dauki abu ka ci har sai ka wanke hannunka. Domin ta hanyar yawan wanke hannu sai ka gusar da kwayar cutar.

Kwayar cutar Corona-virus zata iya rayuwa a jikin tufafi na tsawon sa'o'i shida zuwa sha biyu, yin amfani da sinadaran tsaftace kaya yana kashe kwayar gabadaya.

Shan ruwan dumi yana da tasiri wajen yakar dukkan kwayoyin cuta, itama ma kwayar cutar Corona-virus bata son zafi, zafin daya kai 25° yana kashe kwayar. Don haka hukumomin lafiya suke kira ga jama'a a guji yawan shan kankara da abubuwa masu sanyi (idanma ta shiga jikinka akwai yiwuwar ta mutu saboda zafi). Kwayar cutar ba ta son hasken rana, shiyasa zamu ga tafi tasiri da yaduwa a kasashen da suke da sanyi da wajajen da babu hasken rana sosai.

Masha Allah a halin yanzu a duk duniya ana samun saukin yaduwar wannan cuta, likitoci suna iya bakin kokarinsu kuma a bakin ransu wajen yakar wannan cuta, Likitoci a duniya sun chanchanci dukkanin yabo da girmamawa. Kuma nan da kwanaki masu zuwa lamarin Corona-virus zai zama tarihi a duniya, amma Insha Allah!

Comments

Popular Posts