Skip to main content

Yan Shi'a Sun Kaddamar Da Yaki Da Cutar Koronabairos A Nijeriya

‘Yan’uwa Musulmai Almajiran Shaikh Ibraheem Zakazaky (H) na garin Lafia dake jihar Narasawa sun kaddamar da wayar da kan al’umma akan muhimmancin kiyayewa da shawarwarin Likitoci dangane da cutar COVID-19 da kuma feshin maganin sauro da sauran kwari domin kariya daga wannan cutar.
Wayar da kan al’ummar ya gudana ne a ranar Lahadin 29 ga watan Maris din 2020.

An fara ne daga Kilema aka gangaro ta Kofar Fada aka karkare a bakin tsohon kasuwa.
Masu feshi na feshi masu bayanai na abubuwan da ya kamata a kiyaye suna yi, maza suna yi akan Titi, ‘yan’uwa mata kuma suna shiga cikin gidaje.
An fara lafiya an tashi lafiya an kuma ci gaba yau Litiinin.
ISMA da Harisawa ne suka jagoranci aikin.

Ga wasu hotunan aikin kamar yadda Musa Mahmud Musa ya dauko mana.

 









Comments

Popular Posts