YA KAMATA KA SAN MECECE SHI'A SU WANENE 'YAN-SHI'A KAFIN KA FARA KAFIRTA S


Ba ka San mecece Shi'a a bakin Dan Shi'a ko litattafan Shi'a ba, bilhasali ma daga bakin wadanda suke tsananin kiyayya da Shi'a ka ji mecece Shi'a...
Shin ka taba tambayar Dan Shi'a ko yayi Imani da Allahu Ta'ala.?
Sau nawa ka ji ko ka karanta litattafan Shi'a ka ga menene matsayin Annabi Muhammad(S) a wurinsu.?
Menene matsayin Sayyidina Ali karramallahu Wajahahu a wurin Shi'a ka karanta littafinsu ko ka taba tambayar Malamansu sun fada maka.?
Shin a wane littafin Shi'a ka ga sun tabbatar maka da cewa suna da wani Qur'ani bayan Wanda Annabi Muhammadu(S) yazo dashi.?
Mafi yawan Malaman da suke fada maka mecece Shi'a,suke fada maka abinda suke Kira sharrin Shi'a ce maka suke yi kada ka kusanci 'yan-shi'a,kada ka karanta litattafan Shi'a,kada ka saurari duk wani jawabi nasu,to shi a Ina ya samo sharrin Shi'a.?
Idan dai baka yi tunani ba,Kuma baka yi amfani da hankalinka da basirarka ba wadannan miyagun Malaman sun rinka kada ka kamar Shanu kenan....

Comments

Popular Posts