Uwargidansa Maulana sayyid zakzaky (H): Young Ahmad Snk Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana da mace xaya, wannan kuwa ita ce Malama Zeenatuddin Ibraheem, ita ce mahaifiyar duk ‘ya’yansa, wato daga gareta zuriyarsa ta samu. An haifi Malama Zeenatuddin ne ranar 14 ga watan Ogusta na shekarar 1961, a unguwar Sabon Gari da ke cikin garin Zariya. Sunan mahaifinta Malam Ibrahim, sunan mahaifiyarta Malama Maryam, su huxu ne a wajan mahaifiyarsu kuma dukkaninsu mata, Nafisa Ibraheem, Maryam Ibraheem, Zeenatuddeen Ibraheem da Khadija Ibraheem. Malama Zeenatu ta fara karatun firamare ne a wata firamare ta Mishon da ke Sabon Gari Zariya, daga baya ta koma Firamaren Jafaru, wato St, George Primary School Zaria, daga 1967 zuwa 1973. Daga nan ta tafi “Commercial College, Zaria” a shekarar 1977, ta kammala a 1979, sai ta tafi CAST Katsina, ta shekara biyu a can, daga nan sai ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1981 inda take karanta fannin aikin Banki, amma ba ta samu damar qarasawa ba sakamakon korarsu da makarantar ta yi saboda harkokin addini a sekarar 1982. Daga nan Malama Zeenatu ta tafi karatu a wata “Hauza Ilmiyyah” da ke qasar Iran, daga shekarar 1982 zuwa 1984. Malama Zeenatu baiwar Allah ce ma’abuciyar hidima ga addini da tsayuwa akan hadafi, mace ce haziqa mai tsananin riqo ga karantarwar addini da fikirar Harka Islamiyya. An shaideta da yawan ibada da kishin addini da tsananin tausayawa mata. Insha Allahu topic dinmu nagaba shi ne aure mlm zakzaky da mlm zeenat. Allahu ya faranta mana da gani su mlm elaheey ajib. Free free zakzaky By

Comments

Popular Posts