IDAN KA SAN BABU HANNU KO BAKINKA A ZALUNTAR MALAM ZAKZAKY(H) KADA MUNANAN ADDU'OIN DA MUKE YI SU DAME KA...........!!!
..
Har Yau har gobe bamu San a wane hali Sheikh Turi, Malam Mukhtari Sahabi, Malam Mustafa Lawal Nasidi, Doctor Mustafa Sa'id da daruruwan 'yan-uwa Almajiran Malam Zakzaky(H) suke ba..
Babu mamaki an kashe su,babu mamaki an kone su da rayukansu a gidan Malam Zakzaky(H),babu mamaki an binne su da ransu a ramin da Gwamnatin Kaduna ta binne Mutane sama da dari hudu..
Babu mamaki wadansu daga cikinsu suna tsare a wadansu miyagun wuraren azabtar da Jama'a...
A cikin wadannan Mutanen dana lissafa a sama babu Wanda EFFCC ko ICPC take tuhuma da satar dukiyar al'ummar Nigeria..
Duk cikarsu babu Wanda Sojojin Nigeria ko 'Yansandan Nigeria suke tuhuma da ayyukan ta'addanci a Nigeria...
Babu Wanda ake tuhuma da satar Shanu ko kidnapping...
A cikin wadannan Mutanen babu Wanda ake tuhuma da yunkurin juyin mulki a Nigeria..
Menene laifinsu.? Har Yau har gobe babu Wanda ya Fadi laifinsu daga Gwamnatin Tarayya ko ta Jiha...
Kisan dabbancin da Sojojin Buhari suka yi a Zaria masana harkar tsaro sun Kira shi da massacre ko genocide,sun ce wauta ne da kuma ta'addanci,sun ce zalunci ne da wuce iyaka,sun ce take hakkin bil-adama ne da wauta...
Wai bayan anyi Wannan dabbancin ne wasu daga cikin 'yan-uwanmu Musulmai suka rinka murna da farin-ciki,suka rinka yanka dabbobi suna jinjina da wakoki ga wadanda suka kashe Mutane marasa makami a Zaria, saboda suna Shi'a...
Allahu Ta'ala baya zalunci ya Kuma haramta shi a tsakanin bayinsa.
An zalunce mu,shi yasa muke addu'a cewa duk Wanda yake da hannu ko ya goyi bayan ta'addancin da aka Mana, Allahu Ta'ala ya rusa kasuwancinsa idan Kuma ma'aikaci ne ya rusa aikinsa,idan Mai mulki ne ya kwace mulkin cikin kaskanci da wulakanci...

Comments

Popular Posts