Nigeria za ta kyautata alakarta da isra'ila kan Harlan soji

KO MUTANE SUN GA WANNAN?

Nijeriya Za Ta Kyautata Alakarta Da Isra’ila Kan Harkar Soji

By TANTABARAHAUSA on MARCH 4, 2020

Jakadan Isra’ila a Nijeriya, Shimon Ben-Shoshan, ya ce gwamnatin Isra’ila a shirye take ta kara zurfafa alakarta da gwamnatin Nijeriya wajen magance ta’addanci.

Ben-Shoshan ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Hafsan sojojin kasa na Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ranar Talata a Abuja.

Ya ce, kyakkyawar alakar da ke tsakanin Isra’ila da Nijeriya ta kai shekara 60, inda ya ce a shekarar nan ta 2020 kasar za ta yi bikin murnar cika shekara 73 da kafuwarta.

A cewarshi, komai na tafiya yadda yakamata a abotar kasashen biyu.

“A shirye muke mu kulla alaka ta kowanne bangare. Kamar yadda ka sani, akwai alaka mai kyau tsakaninmu da gwamnatin da ta gabaci wannan a fannin yaki da ‘yan Boko Haram.

“Ina mai tattabatar maka kuna hannun da ya dace,” inji shi.

Jakadan ya yaba wa rundunar sojojin Nijeriya kan kokarin magance matsalar tsaron da ke addabar kasar da suke.

Ben-Shoshan ya ce, zai so wasu manyan jami’an gwamnatin Isra’ila su kawo ziyara Nijeriya, saboda a tsawon lokacin nan an dade ba a yi irin wannan ziyarar ba.

A cewarshi, muna fatan mu ga sun kawo ziyarar kuma shima Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Isra’ila.

Da yake nashi jawabin, Buratai ya jinjina kan daddadiyar alakar da ta ke tsakanin Nijeriya da Isra’ila.

Ya kuma yi godiya ga Jakadan kan goyon bayanshi ga sojojin Nijeriya wajen kokarin da suke na samar da tsaro a kasar.

A cewarshi, Nijeriya ta dade tana  jin dadin alaka da Isra’ila kuma za ta ci gaba da aiki tare da ita.

https://tantabarahausa.com/nijeriya-za-ta-kyautata-alakarta-da-israila-kan-harkar-soji/

Comments

Popular Posts