Cutar yunwa ta fi cutar Coronavirus kisa - Sarkin Musulmi



- Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa wajen inganta rayuwar yan Najeriya
- Sultan na Sokoto ya ce lallai cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da mummunan cutar Coronavirus
- Ya ce a matsayin su na Shugabannin addinai da al’umma, ya zama dole su tattauna wadannan lamura, da kuma ba gwamnati shawarwari
Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa wajen inganta rayuwar yan Najeriya, inda ya ce lallai cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da mummunan cutar Coronavirus.
Sultan wanda ya yi magana a taron kungiyar addinai na Najeriya a Abuja, a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris, ya ce duk da cewar Coronavirus na kashe daruruwan mutane a fadin duniya, “cutar yunwa” shine babban makashinyan Najeriya.
Ya ce: “Akwai wata babbar cuta da ke kashe yan Najeriya fiye da Coronavirus. Wannan cutar ita ce yunwa. Akwai cutar yunwa kuma ta yi lamari. Akwai bukatar ku zaga kauyuka da garuruwa ku ga yadda mutane ke gwagwarmayar rayuwa.

Comments

Popular Posts