Na taba ji Sheikh Zakzaky yana cewa; Allah yanada rundunoni dayawan gaske,da zai iya yakar masu girman kai,

, har Sayyid(H) yake cewa Allah na iya yin amfani kowane irin abu a matsayin rundunarsa, misali kamar;Iska,ruwa,Kudan Zuma,Tururuwa, dss.

Izzar Allah kenan, Cuta kwara daya ya saukar, ba fa rundunar Mala'iku ko rundunar Aljanu ya saukar ba,sannan ba wasu Makamai masu Lonzami ya sako daga sama ba, ba kuma wasu halittu ya saukar ba,aa, Cuta ce guda daya,yau gashi ta fitinar da al'ummar duniya.

Cuta ce guda daya,amma yau kowa na jin tsoronta tun ma kafin tazo Kasar su ko garin su. Akan Cuta guda daya yau gashi kowa ya zauna gida saboda tsoro, andakatar da zuwa wuraren Ibada da kasuwanni, babu zirga-zirga.

Yau da Shugabanka da Gwamnoni da Sakuna, da Soja mai Kisa,kowa na jin tsoron Cutar da bai ganta a zahiri ba, Talakawa da masu dukiya kowa ya firgita. Allah bai zabe wasu yabar wasu ba,ya saukar da Cutar a kasar da suke bautar Shanu,da Masu ganin cewa su kadaine Musulmai wasu kafirai,da masu bautar Rana,ba Musulmi,ba Kirista.

Kowa na jin tsoron Cutar CoronaVirus.

Tsarkin ka,Buwayarka,karfin Ikon ka,ya kara tabbata gare ya Ubangijin Talakai.

Comments

Popular Posts