— Al-Zakzaky Sunana.

Ina zaune cikin gidana tare da iyalaina da wasu daga jama'ana, da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar 12/12/2015 kawai na ji karar harbin bindiga a unguwata.

Na tambaya mene ne? Aka ce wai Sojojin Nijeriya ne suka kawo hari gidana, sun tsaya a nisan kamar kilo mita guda da gidan, suna kashe duk wanda suka gani a kan layin da ke zuwan gidan nawa.

Can suka dan tsaya da harbin, sai wani a cikin mutane na, yace a bashi su je su tattauna da Sojojin nan ko za su ji takamaiman dalilin da ya kawo su suke harbi ba tare da sun wa kowa magana ba.

Bayin Allah hudu daga mutanen da ke gidana suka tunkare su da nufin jin ko me ya kawo ko? Sai kawai suka bude musu wuta suka kashe su. Daga nan suka cigaba da kisa ba kakkautawa tun wannan farko daren har zuwa wayewar garin Lahadi.

Sojojin suka karu a yawa da makamai da Asubahin ranar Lahadi, bayan sun kashe duk jama'ar da ke gidana, suka sakawa gidan wuta ya kwana har ranar Litinin yana ci, gidan ya kone kurmus a yayin da ni da iyalaina da wasu daga jama'ana muke cikinsa.

Sojojin bayan sun kona wasu mutane da ransu ciki har da Yayata yar shekaru 70, suka zo inda nake suka bude wuta a kaina, suka kashe yayana uku a kan idona, suka harbi matata a kirji, sannan suka bude wuta a kaina suka cire kwayar idona da harsashi, suka harbi hannaye da kafafuna, suka ja ni a kan gawar yayana, suka kaini kofar gida, suka daga ni suka saka ji a cikin baro, suna izgili da cewa sun kawo karshena.

Tun a rannan suka tafi da ni, suka tsare ni a barikin soji, suka mai da ni hannun DSS, suka tsare ni a Abuja, suka maido ni Kaduna suka cigaba da tsare ni, yanzu kuma suka mai da ni da matata gurbataccen gidan kurkukun Kaduna alhali muna cikin matsanancin rashin lafiyar da matata bata iya tafiya da kafarta sai da keken guragu, a yayin da ni ban iya walwala sai na gingine wuya na na rufe fuska na.

Yau kimanin shekaru 4 cur da kusan wata hudu ina killace a kurkukun azzalumai ana tsare da ni bisa umurnin Buhari da Elrufa'i. A yayin da Allah Ya kawo annobar da ta tilastawa duniya killace kai da takaita musu walwala da zirga-zirga, ku tuna da cewa ni wadannan azzaluman sun jima da killace ni cikin matsanancin rashin lafiya bisa zalunci.

A yayin da Allah Ya kaddara annobar da ke sa ba a fita sai an rufe fuska ga duk duniya, ku tuna da cewa ni a tsawon shekaru fiye da hudu ban iya fita inda ake iska sai na rufe fuska na saboda gubar da ke cina a jikina da rashin kwarin jikin da tartsatsin harsasan da ke nan a cikin kaina har yanzu ba a cire su ba.

A yayin da ku mutanen duniya kuke neman dauki da agaji a kan cutar da ke addaban azzalumanku da nagargarunku, ku tuna da ni cewa a tsawon shekaru fiye da hudu ina fama da rashin lafiya da raunin harsasai da barazanar shanyewar jiki, da hawa da saukan jini ba bisa ka'ida ba, kuma Buhari da Elrufa'i sun hana ni damar samun kulawar musamman daga likitoci.

A yayin da kuke neman agaji daga Allah akan cutar da ta ke kokarin tilastaku shiga cikin irin Halin da azzaluman kasata suka saka ji a ciki na fiye da shekaru hudu da watanni, ku rika tayani da addu'a akan Allah Ya gaggauta kubutar da ni, ya kuma sa wannan cutar ce ajalin duk mai hannu wajen cutar da ni bisa zalunci da danniya.

Ina muku fatan Allah Ya Baku kariya daga annobar da ke fuskantar duniya na wannan abin da aka kira CoronaVirus. Ina rokon Allah Ya takaita ta, Ya tausayawa raunana. Ya yafe mana.

*Jikina da raunin harsasai ga jini yana kan ci na,
*Jinina ya kan hau ya sauka hakka ma na matata Zeenah,
*Tafiya ko bata iyawa sai a keken guragu Zeenah,
*Sun hana naga likita na, sun tsaurara tsaro na,
*Ga Allah nake kai kuka na a kan duk abin da suke mana.

— Al-Zakzaky Sunana.

Comments

Popular Posts