Tunatarwa

Abunda yake hana mutane da yawa ci gaba shine rashin sanin kan su. Na sha fada, kowane mutum yana da wata baiwa ta musamman wadda waninsa bashi da ita kuma duniya take bukatar ta. Rashin sanin wannan baiwar ne yake dakile ci gabansa. Mutane da yawa sun fi damuwa da ganin ci gaban wasu, suna mantawa da kansu.

Kowane mutum yana da hanyar ci gabansa ta daban wadda ta sha banban da wanin sa. Da yawan mutane suna damuwa da kwafar salon hanyar da wasu suka bi suka samu ci gaba. Suna manta abubuwa da yawa a baya.

"Self-concept" shine yake banbanta wanda yabi wani hanya ya samu ci gaba da mai kwafar sa. Shi mai kwafar wani yana bin hanyar ne don wani ya samu ci gaban. Amma bashi da kwarin gwiwa da yadda da kansa kamar yadda na farko yayi. Sai mutum ya kare a faduwa. Maimakon ya samu nasara sai ya fadi.

Idan ka gane kanka, ka gane baiwar da Allah yai maka sannan ka daina damuwa akan ci gaban wasu ka tsaya akan kanka don samun nasararka, shine ka dauki hanyar ci gaba da sanja rayuwar ka akan damuwa da kanka.

Comments

Popular Posts