A GAGGAUCE

A GAGGAUCE;



Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce Babu Wanda zai Fito da sunan Sallar Juma'a domin yin hakan zai Haddasa Taron Jama'a kuma ta bada umurnin a rufe kasuwanni gaba ɗaya daga Ƙarfe 12 na Daren yau Alhamis Sannan kowa ya tsaya cikin gidan sa domin kiyaye yaɗuwar Cutar Coronavirus.
Hakazalika dokar ta ce Babu wani Ofis ko Shago ko wurin Ibadar da a ka ba Izinin ya Buɗe har sai anji wata Sanarwa ta Daban.
A ƙarshe Sanarwar ta ce, Gwamnati zata yi duk mai yiwu wa wajen Ganin jama'a sun bi doka sau da ƙafa a ƙoƙarin ta na tsaftace jihar Kaduna da ƙasa baki ɗaya daga wannan Annoba.
Da fatan za a kiyaye, Allah ya ƙara mana lafiya

Comments

Popular Posts