Waye Ke Son Ya Temaki Jagora?
Nakasa kirga sau yawan adadin da naji wannan maganan da na keso na fada yanzu kaitsaye daga bakin su Mallam (H). Nafasa yin dogon rubutun saboda na lura 'yan uwa basu cika karanta dogon rubutu ba kwata-kwata na lura da haka.
Ba abin mamaki bane a samu hanyoyi dayawa na temakon amma mafi girma ciki kuma mafi tasiri wajan Allah da su Mallam da al'umma shine kazama na Kwarai, wannan ba ra'ayi bane ko kuma wani hasashe a'a tabbatacce ne.
Zama na kwarai na nufin kazama Na gaske abinso hatta ga makiya, kazama tamkar su Mallam din a 'Dabi'a da Ibada, Kamala, Amana, Gaskiya, Mutunci da Kusanci ina nufin ga Allah Subhanahu.
Ta, wannan hanya ake kama zukatan mutane, da haka-haka Mallam yakama zukatan mutanen farko, kuma dama muna bukatan mutane, dan haka Jagora na bukatan mutane koda basu zama ma'aikata ba amma yazama akwai su koda basu aiki.
Kai, mafi kasawa su zama koda Tausayawa sukeyi to anyi ribaa kan su! Inajin dadi naji an yabi dabi'ar wani dan uwa ace masa me Amana da Gaskiya ne, amma matsalar shi 1 'Dan Shi'a ne! Inason wannan matsalar.
Da haka Annabi ya ribaci dubban Kafiran Makka zuwa ga Allah, kuma yadawo Madina ma yayi! Da wannan gyaran Kai Allah ke yabon shi mafi girman yabo cewa; Lalle ne Kai ( Muhammadu) kana bisa Kyawawan 'Dabi'u.
Idan na zama na kwarai, zan jawo iyaye, kanne, yayu da abokai na, harma da makota, yaya kake tsamani suma su jawo wasu? Ko da 1 yana jawo 2 ne ai lissafi dayawa! Shiyasa wannan al'mari na gyara kai, yake da girma sosai sosai.
Akwai darasi kan haka, akwai Misalai, da littafai kai harma da Addu'o'i game da haka. Allah Kasa Mu Iya. Amin Ya Allah!
Share linkππππ
https://ansarulmahdi.blogspot.com/

Comments
Post a Comment