WALLAHI NI MALAM ZAKZAKY(H) NE RED LINE DIN DA IDAN KA TSALLAKE MUN RABA GARI DA KAI KO KAI WANENE........
Tun dana fara mu'amala da social media ban taba rubutu domin cin zarafin wani malami ko wani mutumi Mai Sarauta ko talaka haka siddan ba...
Ina da abokai da 'yan-uwa na jini wadanda muke da sabanin fahimta dasu, Wannan bai sa na dauke su a matsayin batattu wadanda basa Kan daidai ba,muna mu'amala ta rayuwar yau da kullum,muna tattaunawa da hirarraki akan al'amura dabam-dabam cikin raha da girmama juna..
A Wannan saha ta social media akwai abokai wadanda bamu taba ganin juna ba, sannan wadansu fahimtarmu dabam da tasu,wasu ma addininmu dabam da nasu,amma kyakkyawar mu'amala da girmama juna ya Sanya mukan nemi lambar juna mu rinka gaisawa cikin annashuwa da girmama juna...
Me zai sa saboda son rai da Kiyayya da wani ra'ayi naka sai na rinka cin mutunci da zagin abubuwan da kake girmamawa.?
Tun ina Makarantar secondary ta kwana daga 1990 zuwa 1995 nake bibiyar tare da nazarin da'awar Malam Zakzaky(H) a tsakanin GSSS Gamawa zuwa GSSS Misau,har zuwa babbar makaranta ta Advance Level,har lokacin da na gamsu da cewa Wannan da'awar ita ce mafita a gareni,na kuma sallama mata,ba wani ne yace ga yadda zan Yi ba...
Yaushe kake tsammanin zaka iya raba ni ko nesanta ni da shi,ko Kuma kace min ba a daidai nake ba na girmama ka..?
Wannan da'awar ita na dauka mafita Kuma Ina kallon milestones,don haka idan kana ganin sai na bar Malam Zakzaky(H) zaka dauke ni mutum ko Musulmi to daga yau ka daina tunda na tabbata ba Kai ne Mai rubuta ayyukana na Lada da zunubi ba...

Comments
Post a Comment