Talakawan Nigeria suna ta murna akan Coronavirus nakama manyan kasa
Yayin da a sauran kasahen duniya ake tausaya wa wadanda cutar Coronavirus ta kama, abin ba haka yake ba a Najeriya.
Domin yayin da ake kara samun fantsamar cutar a kasar nan, jama’a masu yawan gaske su na caccakar shugabannin da wannan cuta tw kama a Najeriya.
Daga cikin mutum 51 da ya kamu da Coronavirus a Najeriya, mafi yawan su manyan kasar nan ne, ciki kuwa har da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, Sanata Bala Mohammed, Gwamnan Jihar Bauchi da kuma Kakakin Majalisar Jihar Edo, Frank Okiye.
Akwai kuma dan tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda har yau duk da wasu sun san ko wane ne, ba a fito gar da gar an bayyana sunan sa da hoton sa a kafafen yada labarai ba.
Gwamnoni da yawa sun bayyana cewa sun killace kan su, kasancewa sun yi mu’amala da wasu da cutar ta kama.
Wasu Na ‘Allah Ya Kara!’
Da yawan ‘yan Najeriya na gwasale manyan da suka kamu da cutar Coronavirus, saboda haushin yadda aka yi watsi da inganta harkokin lafiya a kasar nan, aka bar talakawa cikin kunci, talauci da kuma fama da matsalar rashin kula da lafiyan
Akasarin manyan masu mulki a Najeriya sun yi watsi da inganta fannin lafiya musamman asibitoci, suka gwamnace su da ‘ya’yan su da matqn su, su na kwasar kudin hakkin jama’a su na tafiya kasashen waje neman maganin inganta lafiyar su.
Ko Shugaba Muhammadu Buhari da iyalan sa, dukkan su na mai zuwa ko da asibitin Najeriya daya neman magani. Duk Ingila suke ficewa.
Ana jin haushin rashin wuyar lantarki, rashin ruwan sha, rashin kiwon lafiya, kuncin fatara da talauci ga ‘yan Najeriya kusan milyan 180, amma a koyaushe manyan Najeriya na kwashe kudade su na tafiya kasashen Turai nemar wa kan su lafiya.
‘Da A Najeriya Cutar Ta Fara Bulla, Da Ficewa Za Su Yi Su Bar Mu’
Wani mai saida katin waya a wata Plaza da ke a Zone 2, Abuja, mai suna Yusuf, ya shaida Mana a safiyar Laraba cewa, “wallahi da a Najeriya ne sannan cutar ta fara bulla, duk wadannan gwamnoni da minisrocin ficewa za su yi Su bar mu da ita. Tunda dama su ko ciwon kai suka ji, sai su kwashi kudin mu, su fice su da iyalan su.”
Bayanin na sa ya samu karbuwa ga wani mai wankin takalmi da ke zaune gefen sa ya na goge wa qakikin mu jakar sa.
Kasancewa mafi yawan wadanda suka kamu da cutar daga Turai suka ahigo da ita, ya kara bakanta wa wasu ‘yan Najeriya rai matuka.
Sun nuna haushin yadda shugabanni ba su damu da inganta kasar nan ba, sai dai sace kudin kasar nan au fice
Comments
Post a Comment