KAWO HANKALINKU NAN KU JI!
“Duk lokacin da ka ji mutum ko an ce masa Shehi, ko an ce masa Ustazu, ko babban Malami, ko Sarki, ko Suldani na Musulmi, komin girman tinjimemen rawaninsa, komin katon abayarsa, ko mene ne nasa ko dan waye, ko waye, in dai ka ga abin da yake yi yana kokarin ne ya raba Musulmi, to, yana yiwa makiyan Musulmi ne aiki. Ko waye shi! Duk wata magana da zata raba Musulmi, ta ce; wani bangare na Musulmi an kore su daga Musulunci, to, ana yi wa makiya aiki ne.
“Domin addini sassauka ne, ‘La ilaha illalah, Muhammadu Rasulullah.’ Fassara ya na iya bambanta, amma bai fidda mutum Musulunci ba. Wanda ka ga yana kokarin ya fidda mutum, ya fidda shi daga da’irar Musulunci, to, makiya yake yiwa aiki. Kuma wannan da’awar tasa ba zai amfani kowa da komai ba!”
—In ji Shaikh Ibraheem Zakzaky a hirarsa da jaridar RARIYA a 2015.
Comments
Post a Comment