HANYOYIN KARIYAR KAI DAGA ANNOBAR CORONA:
Kasancewar cutar ‘corona’ ta zama annoba ga duniya baki daya. Akwai wasu matakai da kungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana a matsayin yanda za’a yi kokarin kawar da wannan barazana ta hanyar hada hannu da karfe wajen ganin bayan ta.
Akwai matakan da su ke a hukumance, akwai kuma wadanda su ke a daidaiku- wanda kuma hakki ne akan kowa ya zama ya kula da su domin kare lafiyar sauran al’ummar da ya ke rayuwa a tare da su.
- Matakan da su ke a hukumance, sun hada da:
•Testing: (Gwaji ga wadanda ake zargin su na dauke da cutar domin tabbatarwa).
•Isolation: (Ware marar lafiya daga cikin sauran al’umma)
•Contact tracing: (Nemo wadanda su ka yi cudanya da duk wanda aka tabbatar yana da cutar ta hanyar gwaji).
[Gwamnati da ma’aikatan lafiya ke da alhakin ganin cewa duk wadancan abubuwan sun tafi daidai yanda ya kamata. Amma hakan zai yiwu ne kawai idan al’umma sun ba da hadin kai yanda ya kamata].
- Hanyoyin kariyar kai:
1. Wanke Hannu:
Wanke hannu akai-akai da sabulu da ruwa ko kuma man wanke hannu [alcohol containing]. Bayan da kafin cin abinci, shiga toilet*, taba wani abu musamman a waje, dss.. [Zai fi kyau idan mutum ya zama yana yawan wanke hannun shi ne kafin/bayan yin komai].
Wanke ma yara hannu, musamman bayan sun gama wasa, don ba’a san me su ka taba ba*. Idan kuma sun dan yi wayo, ake umartar su su na wankewa akai-akai.
[Wannan shi ya fi komai muhimmanci a duk cikin matakan kare kai, kamar yanda kungiyar lafiya ta duniya ta bayyana].
2. Kaurace ma taba Fuska:
Mutum ya kiyaye taba baki, hanci, ido musamman idan hannun shi ba’a wanke ya ke ba. Saboda mutum bai sani ba, zai iya taba kwayar cuta a wani guri da hannayen shi, idan ya taba daya daga cikin wadancan kai tsaye zai yi ‘transferring’ kwayar cutar ne zuwa inda ya taba.
3. Kiyaye tsafta:
Mutum ya yi amfani da wani abu (mai tsafta) wajen kare hancin shi da bakin shi ya yin da zai yi atishawa ko tari. Bayan ya gama sai ya jefar da kyallen da ya yi amfani da shi (alal misali tissue).. Ko kuma mutum ya lankwasa gwiwar hannun shi, ya yi tarin ko atishawa a tsakanin gwiwar hannun na shi (DAB style). [Natural reflex din mu idan za mu yi atishawa ko tari, mu na sanya tafin hannayen mu ne mu rufe baki da hancin mu. Amma a wannan lokacin akwai yiwuwar mutum ya yi ‘transferring’ kwayar cuta daga baki/hanci/makoshin shi zuwa tafin hannun shi- duk abun da ya taba da tafin hannun ya dora kwayar cutar kenan].
[Wannan matakin na da matuqar muhimmanci saboda mutum zai kare kan shi, da kuma sauran al’umma].
4. Nesantar mutane:
- Mutum ya bada aqalla tazarar kafa 3 (mita daya) tsakanin shi da duk wanda ya ke tari ko atishawa.
Inda abu ya yi tsanani: gwamnati da sauran wadanda abun ya shafa su rufe makarantu, tsayar ta tarurruka/ wasanni dss..
[Wannan matakin na taimakawa wajen yanke hanyar yaduwar cutar tsakanin mutane (cutting down transmission). Sannan ya na taimakawa Asibitoci da sauran guraren kula da lafiya su yi ‘coping’ da yawan ma su fama da cutar. Idan na rage yaduwar ta, an rage yawan wadanda za su je Asibiti neman magani kenan ko?!].
5. Neman taimakon ma’aikatan lafiya:
Idan mutum ya ji alamun ba shi da lafiya, ya ware kan shi na wani dan lokaci kadan. Idan kuma alamun rashin lafiyar ya hada da zazzabi, tari da sarkewar numfashi ne; ya gaggauta kai kan shi Asibiti domin a gwada shi.
[Kar mutum ya ji tsoron zuwa Asibiti a duba shi, idan ya ji irin wadannan alamun musamman idan ya yi cudanya da wanda ya fito daga kasar da su ke fama da cutar; akwai sauran cututtukan numfashi ma su wadancan alamun, saboda haka zai iya zama ba cutar ‘coronavirus’ din ce ta kama shi ba. Amma idan ya qi kai kan shi, ya sanya duk wadanda ya ke tare da su cikin hadari kenan, da ma sauran al’umma baki daya].
6. Kiyaye dokokin ma’aikatan lafiya:
Ma’aikatan lafiya, kasancewar su ne kan gaba wajen yaqi da cutar, su na bada shawarwari akan abubuwan da ya kamata mutum ya yi, da kuma wanda bai kamata ya yi ba. Yana da kyau mutum ya bi shawarar su, domin sun san yanda cutar ta ke- duk shawarar da su ka bada akwai dalilin da ya sanya.
Har wala yau, kungiyar lafiya ta duniya (WHO), ta shawarci mutane akan su ke bibiyar labarai akan cutar, amma daga sahihiyar madogara. Ta haka mutum zai zama ‘up-to-date’ akan duk wani ci gaba (development) akan cutar.
[Da ya ke wannan sabuwar cuta ce, kullum ana samun sababbin bayanai akan ta daga masana a harkar lafiya- ina shawartar mutane da su bibiyi shafukan sadarwa na majalissar dinkin duniya domin ganin bayanai daban-daban akan ta; wadanda ban kawo a nan ba].
Allah Ya kawo karshen wannan cuta haka. Ya warkar da ma su fama da ita, Ya kare al’umma baki daya.
- Najeeb Maigatari.
19/3/2020
[Na kwafo tare da fassara wannan rubutun ne daga shafin kungiyar lafiya ta duniya].
Comments
Post a Comment