Wa Ke Da Alhaki A Ci Gaba Da Tsare Shaikh Zakzaky?
Wa Ke Da Alhaki A Ci Gaba Da Tsare Shaikh Zakzaky?
By - Gwagwarmaya on - March 26, 2020
Shaykh Ibrahim Zakzaky, Malamin addinin Musulunci ne da yake da dimbin mabiya a fadin duniya. Kuma shi ne jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya.
A cikin watan Disamban 2015 ne, ‘yan ta’addan sojojin Nijeriya a karkashin mulkin Manjo Janar Buhari suka kai wa Shaikh Zakzaky da mabiyansa hari a gidansa dake Gyallesu, inda suka kashe dubbai tare da raunata Shaikh Zakzaky da matarsa ta hanyar harbi da harsasai. Sannnan ba ya ga haka suka kama Shaikh Zakzaky da matarsa cikin jini suka tafi da su.
Inda daga bisani suka rushe gidan suka kwashe kasar gidan ma baki daya domin bizne duk wata hujjarsu ta ta’addanci.
Duk da muzaharori a ciki da wajen Nijeriya da aka tsananta ana mai kiran gwamnatin Nijeriya ta saki Shaikh Zakzaky da matarsa, amma gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu. Sannnan ba ya ga muzaharori an rinka rubuce-rubuce da bin hanyoyin da diflomasiya wajen ganin an saki Shaikh Zakzaky da matarsa, amma har yanzu ana ci gaba da tsare su cikin zalunci kuma cikin tsananin ciwon da aka ji musu.
A ranar 2 ga watan Disamban 2016 ne, mai shari’a Justice Gabriel Kolawole na kotu ta 6 dake FHC dake Abuja ya ba da umurnin sakin Shaikh Zakzaky da matarsa ba tare da wani sharadi ba, tare da samar masa da gida a duk inda yake so a arewacin Nijeriya da kuma biyansa da matarsa diyyar take musu hakki akan naira miliyan 50 tare da yi musu rakiya cikin tsattsauran matakin tsaro.
A maimaikon gwamnati ta bi wannan umurnin, sai kuma ta ci gaba da take masa hakki da kashe mabiyansa a duk lokacin da suka fito muzaharar Free Zakzaky a Abuja da sauran jihohi. Wanda ta kaima yanayin da Shaikh Zakzaky da matarsa ke ciki a halin yanzu a kurkukun Kaduna, sam ba dadi.
Shin me yasa har yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta saki Shaikh Zakzaky ba kamar yadda kotun su ta bada umurni? Su wane ne ke da alhakin ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky? Wadansu al’umma ne ba su son a saki Shaikh Zakzaky da iyalinsa? Tabbas zamu iya ce shedaniyar kasa kamar Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila sune ba su son ganin an saki Shaikh Zakzakzaky, a yayin da kasar Saudiyya ke mara musu baya na ganin cewa ba a saki Shaikh Zakzaky ba.
Dukkanin wadannan karfi uku da karnukansu na Nijeriya suna fargaba ne da tsoron yadda addinin Musulunci ke ci gaba da tasiri a Afrika, addinin ma na Musuluncin wanda yake dauke da ruhin gwagwarmaya, shiyasa Haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da tasirin da take da shi a cikin sojojin Nijeriya wajen kisan kiyashin da aka yi a Disambar 2015. Domin da yawan jami’an sojin Nijeriya kasar Saudiyya da Haramtacciyar kasar Isra’ila ke biyasu. Shiyasa suke ganin ra’ayin Shaikh Zakzaky na juyin juya hali da kuma fifita hakkin al’umma, ya zame musu barazana ga munanan manufofinsu.
- Get link
- X
- Other Apps
Comments
Post a Comment