Kungiyar Izala Tayi Amai Ta Lashe!



Wani babban Al'amari daya dauki Hankalin mutane shi ne yanda kungiyar Izala reshen Jos ta fitar da wata sanarwa wacce tayi karo da mganganun shugaban ta Sheik Sani Yahaya Jingir, kwanakin baya. An yita jiyo shugaban kungiyar Izalar Sheikh Sani, yana bayyana cewa wannan Annoba ta Corona Virus karya ce! kuma babu wanda ya isa ya tabbatar masa da hakan.

Ko a ranar juma'ar nan Sheikh Sani, yayi fatali da dokokin Gwaman jihar na kauracewa haduwa waje 1 domin yin Sallar Juma'a, inda tuni Sheikh Sani ya jagoranci Sallar a masallacin 'yan taya dake garin Jos, duk da kuwa barazanar Jami'an tsaro, kuma an sake jiyo shi yana tabbatar da maganan shi akan wannan cuta ta CoronaVirus.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Litinin wacce shugaban Gudanarwa ta kungiyar ya sanyawa hannu Sheik Nasiru Abdulmuhyi ya bayyana cewa; “Kungiyar JIBWIS karkashin Jagorancin Sheik Sani Yahaya Jingir, ta amince da duk wasu matakan lafiya da kariya wanda gwamnatin tarayya ta sanya wajan dakile yaduwar cutar Corona”

Comments

Popular Posts